✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi(00)

Me ke kawo borin jini ne kuma mene ne maganinsa? Domin na taso a gidanmu akwai mai yawan yi. Daga dan Yaya, Jos Amsa: A…

Me ke kawo borin jini ne kuma mene ne maganinsa? Domin na taso a gidanmu akwai mai yawan yi. Daga dan Yaya, Jos

Amsa: A wannan matsala, kwayoyin garkuwar jiki na cikin jini ne ke dimaucewa, su rikice, wato su yi bori, maimakon su yi aikin da ya kamace su, na yakar kwayoyin cuta ko yakar wani bakon abu da ya shigo jini, sai su fara yakar bangarorin jiki. Amma yawanci abinda ke haddasa wannan shi ne shigar kwayoyin cutar jini, ko canjin abinci ko abin sha, da canjin yanayi. A wasu mutanen, idan suka gama yakin wannan bakon abu, sai kuma su fara yakar bangarorin jiki, wato kenan yakan addabi bangarorin jiki daban-daban, kamar yadda muka ce a makonnin baya zai iya taba hanji ya jawo borin hanji, ko fata, wanda muka fi sani, ya jawo kuraje wadanda aka fi gani da ido a sarari.
Cutukan borin jinin kenan iri-iri ne, tunda bangarori daban-daban na jiki suke tabawa. Ya kamata kuma ka san cewa cutukan borin jini sune suka fi kowane irin nau’ukan ciwo yawa a tsakanin ‘yan Adam, domin an san ire-irensu fiye da dari, cikinsu kuwa har da wasu nau’ukan cutukan daji da nau’in ciwon suga na matasa wato (Type I Diabetes) da ciwon sanyin kashi da sauransu.
Bayan wadancan dalilai na sauyin abinci ko yanayi, wasu da yawa suna faruwa ne haka kawai ba dalili. A wasu mutanen kuma akwai gado, wato dama sun gaji kwayoyi masu matsalar, wasu kuma sai sun shiga wani hali na matsi, kamar yadda muka ce. Kai wasu ko cizon kwari ko jin kanshin wani abu da jikinsu baya so, kamar kanshin gyada a masu borin jinin gyada da aka fi gani a turawa, zai iya kawo jininsu yayi bori, da ma sauran abubuwa da za su sa jiki ya ga canji. Idan mutum yayi sa’a wadannan kananan halittu na jikinsa ba masu bori bane, to kusan zai iya zama lafiya a ko wane irin hali ya samu kansa, domin akwai wadanda kowane irin hali suka samu kansu a ciki jikinsu ba ya nunawa.
Wasu nau’ukan borin jini marasa tsanani sukan yi sauki cikin mintuna, kamar wanda sinadaran wasu kwari masu cizo kan sa; wasu cikin ‘yan kwanaki, kamar cin wani nau’i na abinci da jiki kan gani a matsayin bakon abinci; wasu kuma sai an yi makonni suke lafawa. A wasu sai an dan sha magani na ‘yan kwanaki, wasu kuma ba ma sai an sha ba da kansu suke lafawa.
Misalan sauran cutukan borin jini masu karfi irin wannan sune masu kama gabobin jiki wato ciwon sanyin kashi na arthritis ko hanji kamar Inflammatory Bowel Disease, da kuma masu iya kama sauran sassan jiki kamar hanta, ko koda, ko makoko da sauransu.
To da yake kwayoyin garkuwar jikin mutum tana cikin jikinsa dindindin, babu wani magani a likitance da aka sani mai warkar da wannan ciwo gaba daya, sai dai masu sa borin ya lafa, wato masu rarrashin kwayoyin su daina bori. A mafi yawan mutane masu matsalar, idan sun sha yakan lafa kuma ba zai sake tashi ba sai abinda ya jawo borin ya sake faruwa, kamar shan madara a masu borin jini na shan madara. A wasu kuma sai sun dade suna sha na tsawon watanni sa’annan yakan lafa, kamar masu borin hanji, a wasu kuma sai dai su ci gaba da amfani da su magungunan har tsawon rayuwa kamar irin masu ciwon sanyin kashi. Don haka magungunan suna da dama kuma sun danganta da karfin matsalar.
Idan mutum na yawan samun borin jinin kamar yadda ka ce a gidanku akwai mai samu, sai ya je an duba shi a wani asibiti mafi kusa a tabbatar borin jinin ne sa’annan ake rubuta magani, domin ba irin magungunan da za a fada ka je kyamis kawai ka saya bane irinsu Panadol, wadannan suna da karfi. Kai a wasu ma idan abin ya tashi saboda karfin matsalar, har suka suma, idan ba a musu allurar borin jini ba zarcewa suke.
Nima dai likita duk bayan kwana biyu-biyu sai na yi gudawa, an yi binciken an yi binciken na asibiti ba a gano komai ba. Ko nima dai irin wannan matsalar ce da ni ta borin hanji?
Daga Habiba M.
Amsa: E, to da yake mun ce matsalar inflammatory bowel disease ko borin hanji, wadda kuma iri-iri ce, ta fi kama mata, ta iya yiwuwa matsalar ce.
Amma dai ba a karamin asibiti ne zaki tsaya da neman musabbabin gudawarki ba. Ki daure ki koma su asibitin da suka yi binciken su tura ki babban asibiti wajen kwararrun masu duba matsalar ciki wato GIT, sune za su duba gwaje-gwajen su bada zance guda na karshe, na cewa e, ko a’a kaza ne. Da fatan za a daure.
To likita ni ma fa ina yawan samun zafin jiki, musamman a tafukan hannu da na kafa, da zafi a cikina, duk dai ba dadi. Ko akwai magani?
Daga Murja A.
Amsa: To duk dai kanwar ja ce, da yake akwai cutuka da dama masu sa irin wadannan alamu da kika zayyana, watakil kema sabuwar mai binmu ce a wannan shafi. Ita waccan mai tambaya a kan gudawa ta daure ta je asibiti an dubata an mata gwaje-gwaje amma ba a ga komai ba, amma ke kuma baki fada cewa ko kin je an yi aune-aune ba ko ba a yi ba. Wadannan aune-aune da gwaje-gwaje sune ginshikin aikin likitanci, domin idan ba a gane matsalar mutum ba da baki, da an yi gwaje-gwaje a kusan kashi 90% ake gano matsalar. Don haka kema shawara a nan itace a daure a samu ko da karamin asibiti ne inda za a iya gwaje-gwaje a fara da nan tukuna, idan an dace a gano matsalar a nan to, idan ba a dace ba ki bukaci su turaki gaba. Haka ake yi.
Ni likita mai ciwon tarin TB yana warkewa kuwa?
Daga Abubakar Wawar Kaza
Amsa: Mallam Abubakar kusan a iya cewa wanda ya sha maganin ciwon TB na tsawon watannin da aka bashi ya kashe duk wata kwayar cutar TB ke nan da ke jikinsa. Kai zai ma fi irinmu masu lafiya tabbas din cewa babu kwayar cutar TB a jikinsa, domin mu da kake ganinmu masu lafiya, da yawanmu akwai kwayar cutar TB a jikinmu amma a nannade a cikin cikin kwayoyin garkuwar jikinmu da ake kira monocytes, musamman ma wadanda aka yiwa allurar riga-kafinta tun suna jarirai, to amma bata kawo mana matsala saboda kamar an garkameta ne a gidan yari in dai wadannan kwayoyin garkuwa na zaune lafiya. Da sun samu matsala ne suke sakin kwayar cutar ta kawo tari da zazzabi da rama da sauran alamun da ake gani.