✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan sama da mutum 100

Masu zanga-zangar sun koka kan yadda hare-haren 'yan bindigar ya durƙusar da harkar noma.

Wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, sun yi zanga-zangar lumana tare da neman gwamnati ta ɗauki kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankin.

Zanga-zangar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Laraba.

Jama’a da dama sun halarci zanga-zangar; wasu a kan babura, wasu a cikin motoci, wasu kuma a ƙafa.

Kuma sun taru a ƙofar gidan gwamnatin Jihar da ke Gusau domin nuna damuwarsu.

Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe.

Mazauna yankunan sun ce sama da mutum 100 ’yan bindiga suka kashe a baya-bayan nan.

Wani daga cikin masu zanga-zangar, Malam Abubakar Abdullahi daga ƙauyen Fegin Mahe, ya ce ’yan bindiga sun kashe ’yan uwansa da dama, sannan kuma sun sace musu kaya da darajarsu ta haura Naira miliyan ɗaya, ciki har da buhun taki guda 500.

Hare-haren sun hana manoma yin aiki a gonakinsu, saboda rashin tsaro a yankin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Gusau, Abubakar Iman, ta bakin wakilinsa Aminu Wakili Mada, ya ce ya fahimci ƙorafin jama’ar yankunan.

Ya tabbatar da cewa gwamnati tare da jami’an tsaro suna aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya, kuma za a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wuraren da suka fi fama da matsala nan ba da jimawa ba.

Yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ci tura domin bai amsa waya ba.

A wani labarin kuma, jami’an tsaro sun ceto mutum 11 da aka sace a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

An sace mutanen ne a ƙauyen Kaibaba da ke gundumar Turba a Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.

An miƙa su ga Gwamnatin Jihar Sakkwato a ranar Laraba.