Wai da gaske zama da yunwa ne ke kawo ciwon olsa?
Daga Usman, Abuja
Amsa: Eh, zama da yunwa a wadansu yana daya daga cikin abubuwa masu jawo olsa, tunda olsa abubuwa da dama ne ke jawot a, har da kwayoyin cuta da yawan sinadarin acid a ciki da zama da yunwa din ma da cin yaji da yawa, har da yawan shan kayan tsami kamar barasa da burkutu, ko abu mai gas da sauransu.
Shin shan yaji yana da amfani ga lafiya ko kuma a’a?
Daga Khalifa Sani Pandogari
Amsa: Eh, shan yaji zai iya amfani ga wadansu, sa’annan ya iya sa illa ga wadansu. Misali, akwai sinadarin bitaman C a cikin barkono, wanda zai iya amfani, to sai dai kuma akwai wadansu wadanda zafinsa zai iya sa musu gyambon ciki wato olsa.
Ina fama da ciwon ciki da ke zafi har gadon baya. Idan na je asibiti aka ba ni magani yakan yi sauki amma bayan kwanaki sai ya dawo? Wani lokaci idan na tashi zan ji jiri kamar in fadi. A ba ni shawara.
Daga Sadiya Karaye da Rukayya Ahmad
Amsa: Shawara ita ce da alama ciwo yana ci gaba da muku illa wanda hakan na nufin watakila matsalar ta fi karfin asibitin garinku, sai kun fito babban asibiti a birni.
Ina da ciwon olsa amma kullum ina shan maganin olsa, shin shansa kullum ba wata illa ne?
Daga D. M
Amsa: Eh, babu illa in dai likita ne ya duba ka ya ce ka rika sha haka a kullum. Idan kuma gaban kanka kake to kai ma ka san sauran.
Na ga shuwaka ita ma ganye ce mai daci. Ke nan ita ma cinta da yawa zai iya illata hanta ne?
Daga Amina Danfuloti
Amsa: Eh, ita shuwaka idan ana ci daidai misali tana da fa’ida ga ciki har ma da hanta, amma idan aka yawaita ci, hanta za ta iya shan wahala wajen sarrafa dacin.
Wane abinci ne mai ciwon basur zai daina ci?
Daga Ilyasu Wakili Akuyam
Amsa: Duk wani abinci mai sa bayan gida tauri, shi mai ciwon basur zai guje. Amma ba shi ne magani ba, maganin basur sahihi shi ne tiyata
Ina samun ciwon kai idan ina cin nama ko gyada ko kifi. To hakan yana da nasaba da typhoid?
Daga Isa Ibrahim Jos
Amsa: In dai tuntuni kake samun haka to ba typhoid ba ne watakila borin jini ne wato allergy, domin duk nau’in abincin da ka lissafa nau’in protein ne. To amma ba a cika samun borin jini a dukkan nau’in protein ba, sai dai daya, kamar wake kadai ko kifi kadai amma ba duka ba.
Idan kuma da ba ka samun irin wannan ciwon kan sai a yanzu to watakila sai ka je an duba ko akwai typhoid din. Shi ma ba wai saboda nau’in abincin ba, a’a saboda ka ambaci ciwon kai.
Da gaske ne shan shayi akalla sau uku a rana yana kara lafiya? In haka ne wane shayi ya kamata a rika sha?
Daga Matar BZ Kauran Namoda
Amsa: A’a ba gaskiya ba ne a ce shan shayi da yawa a rana zai kara lafiya. Shan shayi sau daya ma idan aka sha mai amfani kamar koren ganyen shayi wato green tea ya wadatar.
Ko ya dace mutum ya ki shan ruwa alhali yana jin kishirwa don gudun yawan fitsari?
Daga MSS Deidei
Amsa: A’a bai dace ba, tunda kishirwa hanya ce da jiki ke nuni da cewa jiki na bukatar ruwa.
Na kasance ko na fita aiki da safe da hantsi ya yi dole sai na samu wuri na kwanta kana nake jin dadin jikina. Shin hakan akwai matsala?
Daga Sa’idu Sabga, Legas
Amsa: A’a ba wata matsala yanayin jikinka ne ko kuma a yanayin irin abincin da kake karya kumallo da shi ne.
Duk lokacin da na jima zaune idan zan tashi sai jiri ya rufe mini ido.
Daga Abban Taslim Sani
Amsa: Duk mai samun irin wannan sai ya je an binciki lafiyarsa, domin alamun matsala ce.
Abokina ne kullum yana dakin karatu yana karatu amma da ya shiga dakin jarrabawa sai ya manta komai. Shin wane irin ciwo ne wannan?
Daga Sadeek Balarabe
Amsa: Eh, ana samun irinsu, bambancin halitta ko fahimta ne, wato bambancin karfin kwakwalwa. Ai a kowane aji a makaranta akan samu irinsu. Akwai wani tsari na musamman da akan yi wa irinsu wajen koyarwa a kasashen da suka ci gaba don taimaka musu.
Mu mutane ne marasa kauri shi ne muke so mu san irin abincin da za mu rika ci domin nu yi kauri
Daga Umar Shehu da Auwalu Musa da Maikudi 94, Bichi
Amsa: Ku kun rubuta kuna son kiba, ni na rubuta ina son ku yi kauri. Kada ku nemi kiba, ku nemi kauri. Kiba a abinci mai maiko wato fat ake samunta, kauri kuma abinci mai gina jiki wato protein ake samu. Don haka sai mutum yana cin abinci mai gina jiki a-kai-a-kai zai yi kauri.
Amma duk da haka idan mutum ba ya da gadon kwayoyin halitta masu sa kauri, wato idan a duk danginsa samun mai jiki sai an tona, to da wuya ya yi jiki ko me zai rika ci.
Me ke kawo a ga wadansu hannayensu rudu-rudu duk jijiyoyi sun fito?
Daga Garzali Ibrahim Darmanawa
Amsa: Idan na fahimce ka irin tashin jijiyoyin nan su kumburo kamar a jikin karfafan mutane ko? In dai wannan ne ba matsala. Amma idan a kafafuwa ne suke firfitowa kuma launinsu na bayyana yana da kyau likita ya gani ya tabbatar ba ciwo ba ne.
Ina yawan tofar da majina ta baki koda ba na mura. Ko hakan akwai matsala?
Daga A.A Danzomo
Amsa: A’a ba komai, wadansu haka halittarsu take suna da yawan sarrafa majina. A wasu lokuta ma kwayoyin cuta ne ke sa sarrafa majinar, sai su shige ka ba ka ma san jiki ya fitar da su ba ta hanyar majina. Sai dai kawai a rika kiyaye yadda ake tofar da ita.