✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amon-takun tunkun ambaliyar aman-teku

Amon-takun tunku Aman-teku Ambaliyar akwaku Aringizon arafku Aron-aku   A murtuke A mutsuttsuke Ai ta make-make An samu lasisin yanke-yanke Ana son doke-doke   Aika-aika…

Amon-takun tunku

Aman-teku

Ambaliyar akwaku

Aringizon arafku

Aron-aku

 

A murtuke

A mutsuttsuke

Ai ta make-make

An samu lasisin yanke-yanke

Ana son doke-doke

 

Aika-aika

Soke-soken suka

Some-somen sussuka

Sassafar sukuwar sauka

Alamta alamu haka-haka

 

Kwantara gora

Zaurancen zantukan ’yan zara

Karafkiyar karon kariyar kwantara kara

Bugi-in-bugar birni da karkara

Jimamin jamhurun jiran jagora

 

Zance ne na uwar daka

Bambamin huda baraka

Carin carar caccaka

Dagar dungun dugu-dugun duka

Warware tufkar hadaka

 

Dauke-dauken hankaka

Maida dan wani naka

Sunkurun satar shirwa

Salon surutun shewa

Turnukun turka-turka

 

Kulkin kwalawan kwanta-kwanta

Kokarar karafkiyar karata

Kwance-kwancen kuntata

Kwaramniyar kullata

Kumburin kasurar kawanyar karanta

 

YankinYaro-Baba

Hauron-Baba

Haurobiba

Hargowar haramben haraba

Hasafin hatsin tsaba

 

Damisar damushere

Damon duman dundumin dare

Dagar dara daron dare-dare

Digiriren dagogwaragon derere

Dawainiyar daure-daure

 

Kwatanceceniya

Ka-ce-na-cen kacaniya

Kankambar kwaramniya

Karajin kin-jin kiriniya

Kokarin karfa-karfan kiren karya

 

Hisba

Hasafin haraba

Haruffan harsashin harbi harba

Husumar haifar da ukuba

Haihata-haihata haba-haba!

 

’Yan uwantaka

Ko fatattaka

Kakarin karkata

Kullafucin kullata

Zawarcin zalamammun zarata

 

Shegantakar shammata

Shashancin shingen shagalta

Hange-hangen hankalta

Balgace-balgacen balbalta

Kuntunguilar karime-karimen kamfata

 

Kundin kunshe-tushe

Kwance-kwancen kwashe-kwashe

Kashi-kashin kashe-kashe

Cika-cikin cushe-cushe

Romon rummacen rashe-rashe

 

Haurobiyawa

Arewatawa

Kadawa

Yammatawa

Gabasawa

 

Kowa dai ya hankalta

Mu daina yi wa juna mugunta

Mui masalaha mu daidaita

Kar shaidanu su sa mu daidaita

Zumun zaman lullumin lumana kar a lahanta

 

Hauhawar hargowar haramta bobon bokoko a yankunan Arewatawa, musamman a yankunan Arewatan Gabashin Haurobiya, tare da garkuwar gagara-kuwwa a yankin Arewatawan Yammacin Haurobiya, daukacin wadannan al’amura su suka ingizo Amon-takun tunkun  Aman-tekun Ambaliyar akwakun Aringizon arafkun Antayowar awon aron aku a yankin Yaro-Baba. Kuma kowa na da masaniya kan yadda aka yi ta fafutikar kafa jami’an dakon dabbar dawa tukkun tagiya bugu da kari a daukacin fadin jihohi.

Watsattsaken jirkice-jirkicen jirwayen jaridu da makalutun makalun mujallu da akwakun kwakwazo da dodannin hotuna masu wuntsila-gudi-gudi, duk sun baje wa Haurobiyawa yadda  yankin Kudancin Yammacin Haurobiya ke ta fuffukar fafutikar kafa turken DAMISAR DAMUSHERE, don haka kowa ke ta ce-ce-ku-ce kan tashin tashinar tashen DAN AKUYAN NAN YA SHIGA RUMBU, sai ku buge shi damusherere.

Hakika daukacin Haurobiyawa, musamman wadanda ba su fito daga yankin da aka kafa turakun takun tunkun Amon-tunkun Aman-teku ba, kowa da yadda ya fasko shirin shiga Sharon tsirin tsaurin tsaro, wato dai ana iya cewa: akwai shegantakar shammatar shashancin shingen shagaltar hange-hangen hankaltar balgace-balgacen balbalta a kuntunguilar karime-karimen kai-kawon kumfar kamfatar karmami.

Su kuwa jagororin al’ummar tuni suka hau dandamalin daddale dalilansu da cewa:  sun kafa turakun Damisar damusheren damon duman dundumin daren dagar dara daron dare-daren digiriren dagogwaragon dereren dawainiyar daure-daure ne don kawwame dukiyar al’ummarsu a lullumin lumanar liyafar rayuwar rayuka. Sannan sun yi kwatanceceniyar ka-ce-na-cen kacaniyar kankambar kwaramniyar karajin kin-jin kiriniyar kokarin karfa-karfan kiren kare-karen karyar Hisbar hasafin harabar harhada haruffan harsashin harbin harba-harbar husumar haifar da ukubar haihata-haihata haba-haba!

Bisa la’akari da takaddamar turka-turkar tokarar takun tunkun tunkudowar teku, akwai bukatar lallai Haurobiyawan Arewatawa da Kadawa da Yammatawa da Gabasawa su yi mai yiwuwa wajen kauce wa hauka-haukan hantarar hukuma don tabbatar da kimar kundin kunshe tushe ko kwance-tushe?

Watakila sun fasko yiwuwar LAULAYIN ALAYEN LAUYE-LAUYE da ka iya haifar da kwance-kwancen kwashe-kwashen kashi-kashin kashe-kashe cika-cikin cushe-cushe romon rummacen ragon Romawa rashe-rashe

Lallai sai a hanzarta a yi ’yan gyare-gyare, amma ban da kagen kare-kare da ka iya haifar da GYARE-GYARE IRIN NA GYARE DA KUREGE.

Kundin kunshe-tushe dai ba ya bukatar kwashe-kwashen kashin kashe-kashen cushe-cushe romon rummacen rawunnan RUFA-RUFAR RAMUWAR-FANSA, tamkar yadda lamurra suka kasance a KUDANCIN IFIRIKIYYA; Ko RUWAN DAREN RUWAN RANDAR RUWANDA, muna sane da hautsinin Tutsun Tsutsi da husumar hutun Hutu. A kundin labaran da, da na yanzu sai mu yi bitar bin-kadin langabun Laberiya da sukuwar sululun Saliyo. Ga tada kayar bayan Auzinawan Arewacin Niyyar-jari, inda aka baje bujen buzuzun buzu buzu-buzu. Daukacin wadannan al’amura da aka bijiro da su a matsayin misalan jimurdar jikata jikkunan jama’a a daukacin fadin Ifirikiyya sai su zama izina ga Haurobiyawa, ko don su yi kokarin dorewar lullumin lumana lullum.

Matukar masu BUKATAR BABAKEREN BUKKAR BARARRAJEWAR BARAGURBI sun doge, hakika za su burge idan har suka mayar da GAGARARRU GYARARRU, maimakon a jinka musu ta’adar tada kan addar adawar tsoratarwar tsoro. Idan kuwa sun murtuke, sun matse, sun motse an mutsuttsuke ana ta make-make don samun lasisin yanke-yanke da doke-doke, to kowane yanki damarsa ce a tsarin DAMON-KURAR-DIYYA ya dinga ’yan daba da ’yan sara-suka, su ma su GIRGIZA GARIYO, a dan motsa ko a ji dadin yamutsawa.

Masalaha dai kowa ya tare a GUDUNMAR GUDUNMUWAR GAMAYYAR GAMA-GARIN al’umma, masu himmar tarairayar tarayya, don gudun ka da magabta su yi mana kawanya, har a zo ana ta kayya-kayya. Karshe a karke da jefa azargagiyar zarge-zarge kan wane da wane a wuni-wunin wa-ka-ci-ka-tashi mai mamakon muni.

Gwamnatin Baban-burin-huriyya wajibi ne a yi wa wannan  tufka hanci, don gudun ka da a jefa jama’a cikin kunci. Mu kuwa al’ummar kasa mu tabbatar da ’Yan uwantaka, tare da kauce wa fuffukar fatattaka juna, ko kakarin karkata kullafucin kulla-kullar kullatar zawarcin zalamammun zarata. Kowa dai ya hankalta, mu daina yi wa juna mugunta; mu yi masalaha mu daidaita ka da  mu bari shaidanu su sa mu daidaita zumun zumuntar zaman lullumin lumanar liyafa lakume laifuka, don haka mu kiyayi lahanin la’antar lamunin laftun lafkewar langabewar lahanta. Mu yi watsi da hayagagar ayaga, mu bi doka ka da kowa ya koka, a yi ta kokarin tabbatar da adalcin adala. Don haka kowa ya kula ka da a jefa al’umma halin kila-ka-kala.

Idan na-zomo ya ji, to gangar jiki ta tsira, ta yadda ba za a yi mata tsirara ba, amma idan ya ki ji, to ba a ki gani ba; kuma jikkuna ba za su ki jikkata ba. ‘Jiki dai magayi bankar bukin dan Korau!’