Aminiya na neman ma’aikata a bangaren Aikin Jarida na Zamani (Digital Journalism).
Idan kun lakanci aikin jarida da amfani da kafafen sada zumunta wajen yada labarai sannan kuna bibiyar abubuwan da ke faruwa yau da kullum, to wannan dama ce a gare ku.
- Angon Disamba: Yadda rasuwar matashi ta girgiza mutanen Facebook
- DPO ya lashe musabakar Alkur’anin ’yan sanda ta farko a Kano
Aikin ya kunshi bincike, zakulo labarai da tantance su, gami da bibiyar al’amura da fahimtar harkar yada labarai ta hanyar kafofin zamani.
Dole ne mutum ya kasance ya iya rubutun Hausa, kuma yana iya Ingilishi, ya san abin da masu karatun labaran Hausa suke so, sannan ya mallaki shaidar karatu ta akalla digirin farko ko HND.
Aikin kwantaragi ne a Abuja, ya kuma kunshi yada labarai ta intanet da kafofin sada zumunta.
Dama ce ga maza da mata; wadanda suke ganin sun cancanta daga ko’ina, sai su aiko da takardunsu ta [email protected], a rubuta ’Yan Jaridar Zamani a wurin Subject. Za a rufe karbar takardun ranar 3 ga watan Dismba, 2021.