✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta mayar da ilahirin ’yan Bayelsa ’yan gudun hijira – Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce yawan ambaliyar ruwan da jiharsa ta Bayelsa ta fuskanta a bana ta mayar da kusan ilahirin mutanen cikinta…

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce yawan ambaliyar ruwan da jiharsa ta Bayelsa ta fuskanta a bana ta mayar da kusan ilahirin mutanen cikinta ’yan gudun hijira.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron godiya na musamman na jihar na shekara-shekara da ya gudana a Yenagoa, babban birnin jihar, ranar Laraba.

Jonathan ya ce tuni ya tattauna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo, kan halin da mutanen ke ciki da nufin tallafa musu.

Aminiya ta rawaito cewa hatta gidan tsohon Shugaban da ke garin Otuoke a Karamar Hukumar Ogbia, sai da ambaliyar ta mamaye shi.

Tsohon Shugaban ya kuma jinjina wa tsohon Gwamnan Jihar, Seriake Dickson saboda gina katafariyar cibiyar bauta tare da kirkiro da taron godiyar na shekara-shekara, yana mai cewa jihar ba za ta iya cim ma komai ba in ba taimakon Ubangiji.

Ya kuma yaba wa Gwamna mai ci, Douye Diri, saboda ci gaba da shirya taron.

Jonathan ya kuma roki Gwamnatin Tarayya da ta tallafa wa mutanen jihar la’akari da iftila’in da ya fada musu, inda ya ce yana da kwarin gwiwar samun tallafi saboda yadda ya nemi a tallafa musun.

“Ina tausaya wa dukkanku kan yadda kuka yi fitar farin-dango a yau, duk da halin da kuke ciki, wannan abin sha’awa ne,” inji Jonathan.

%d bloggers like this: