Matafiya na shan bakar wahala kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja daidai Koton Karfe sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye hanyar.
A cewar wakilinmu, ruwan da ya yi ambaliya ya mamaye zuwa bakin sabuwar gadar da ake ginawa a garin Koton karfe wanda ya hana motoci bin hanyar a ranar Litinin.
- Ambaliya ta ci mutum 3, wasu 50,000 sun rasa muhallansu a Kogi
- Ambaliyar ruwa: An tsinci gawarwaki 15 cikin kogi a Maiduguri
Hakan ya haifar da cinkoson motoci manya da kanana da ke kokorin su wuce amma abin ya faskara.
Lamarin ya kara dagulewa ne a lokacin da wasu manyan motoci suka makale a ‘yar hanyar da ake ratsa wa a wuce.
Wanda hakan ya jefa motoci da yawa da sauran matafiya cikin tsaka mai wuya sakamakon gaza darawa ko’ina daga inda suke.
Haka kuma matafiyan ba su da damar juya wa baya saboda cinkoso, da ta sa daya hannun ma wasu motocin sun toshe.
Wani mutum da ya samu nasarar juyawa ya dauki hoton bidiyo dandazon motocin da suka cika hanyar, ya kuma yi bayanin irin wahalar da ya sha kafin ya juyo.
Jihar Kogi na daya daga cikin jihohin da ambaliyar ruwa ta fi shafa, sakamakon kasancewar kogin Binuwai da Neja da suka hadu a Lokoja, suka kuma cika da ruwa suka tumbatsa a wannan shekarar.