Mutum shida sun rasu bayan 239 sun kamu da cutar mai da gudawa sakamakon gurbacewar ruwan sha da ambaliyar ruwa ya haifar a kananan hukumomi biyar na Jihar Gombe.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Habu Dahiru, ya ce mutum shidan sun rasu ne a unguwar Kagarawal da ke Gombe, bayan barkewar cutar a kananan hukuomin Balanga da Yalmatu Deba da Nafada da Funakaye da kuma Gombe.
- Mutum 3 sun mutu a hatsarin mota a Gombe
- An yi wa jarirai 191,222 rajistar haihuwa cikin shekara 1 a Gombe – NPC
A bayaninsa ta bakin Babban Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin Farko, Dokta Abdurrahman Shu’aibu, kwamishinan ya ce, tuni hukumar ta dauki matakan dakile yaduwar cutar ta hanyar samar da cibiyoyin kula da wadanda suka kamu.
Ya kara da cewa, za a gudanar da feshin magani a rijiyoyi da burtsatse a wuraren da cutar ta bulla, sannan za a rarraba kwayar maganin tsaftce ruwa gida-gida domin dakile yaduwar cutar.
Mutane kimanin 2,373 ne suka kamu da cutar kwalara a wata shida da suka wuce a jihar.