✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe

Gobarar wadda ta tashi da rana tsaka, ta yi saurin yaɗuwa zuwa gidaje uku, inda ta ƙone su kurmus.

Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira.

Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin sake farfaɗowa daga wannan masifa.

Gobarar wadda ta tashi da rana tsaka, ta yi saurin yaɗuwa zuwa gidaje uku, inda ta ƙone su kurmus.

Hukumomin yankin har zuwa yanzu ba su bayyana ainihin dalilin tashin gobarar ba, yayin da waɗanda abin ya shafa suke zaune ba tare da matsuguni ko abinci ko kayayyakin amfani na yau da kullum ba.

Malama Sakina, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, cikin kuka tana mai bayyana cewa,  “Mun rasa komai. Babu wanda ya taimaka mana lokacin da gobarar ta tashi. Muna buƙatar taimako, musamman daga gwamnati da masu taimakon jama’a, domin mu sake tsayuwa. Kowa ya san halin ƙunci da ake ciki yanzu.”

Wani wanda gobarar ta shafa, Yakubu Baba Gombe, ya bayyana damuwa kan jinkirin da jami’an kashe gobara suka yi wajen isowa wurin. inda ya ce, “Lokacin da suka iso, komai ya riga ya ƙone.”

Iyalan da abin ya shafa yanzu haka sun dogara ne ga taimakon al’umma don samun tallafi na gaggawa. A halin yanzu kuma, mazauna yankin suna kira ga hukumomi da su gudanar da bincike kan lamarin tare da ɗaukar matakan kariya daga aukuwar irin wannan gobarar a nan gaba.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin ya ji ta bakin hukumar kashe gobara kan wannan gobarar amma lamarin ya citura

Wannan iftila’i ya bar mutane cikin baƙin ciki, yayin da iyalai ke roƙon taimako domin sake gina rayuwarsu. Ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara bai yi nasara ba.