Ambaliyar ruwan sama ta salwantar da kadarori na kai miliyoyin kudi a Kafachan, jihar Kaduna
An fara ruwan saman mai karfi ne tun daga misalin karfe 11:00 na daren Tarala zuwa wayewar garin Alhamis.
Da suke magana da wakilin Aminiya, wadanda abun ya shafa sun ce, ambaliyar ta faru ne saboda ruwan da aka dauki awanni ana yi kuma magudanan ruwa suka cushe.
Sun kuma yi kira ga gwamnatin karamar hukumar da ta jiha da su kawo musu dauki saboda asarar da suka yi ta kaddarori da amfanin gona da gidajensu.
Wuraren da ruwan ya fi barna sun hada da Titin Jagindi da bayan Hedikwatar ‘yan sanda da Hayin Gada da kuma bangaren Titin Kalaba.
— ‘Jama’a su tashi daga hanyar ruwa’
A nata bangaren, Gwamnati Jihar Kaduna ta yi kira ga masu gidaje a gabar Kogin Neja da su tashi domin su tsirar da ransu da dukiyoyinsu.
Hukumar Agaji ta Jihar (SEMA), ta kuma yi kira ga mutanen da suka yi gini hanyar ruwa da su kwana da shirin ambaliyar ruwa saboda duk wani kogi da ake da shi makil yake da ruwa.
Sakatariyar Hukumar, Maimunatu Asabe Abubakar, ta kuma shawarci mazauna wurare masu hadari da su sauya ungwanni domin kare rayuwarsu da dukiyoyinsu.