✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta rushe gadar ta haɗa Arewa da yankin Kudu maso Yamma 

Matafiya daga Kudu da Arewa sun kasa maƙale sakamakon rushewar muhimmiyar gadar

Matafiya sun maƙale bayan ruwan ambaliya ya yi awon gaba da babbar gadar da ta haɗa yankin Arewa maso Yamma da yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Gadar wadda ta haɗa jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara da yankin Kudu maso Yamma ta rushe ne ranar Litinin a a Ƙaranar Hukumar Keɓɓe da ke Jihar Sakkwato da kuma Shanga a Jihar Kebbi.

Rushewar wannan muhimmiyar gada a sakamakon mamakon ruwan sama ta hana matafiya daga jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara isa zuwa yankin Kudu.

Hakazalika matafiyan da suka taso daga Kudu maso Yamma zuwa Arewa ta Yamma sun maƙale sun kasa tsallakawa zuwa jihohin guda uku.

A yayin ziyarar gani dacido da ya kai wurin, Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa rushewar gadar za ta haifar da mummunan matsala ga harkokin tattalin arziƙin manoma da ’yan kasuwa a faɗin Najeriya.

Gwamnan ya yi kira ga Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa da ta gaggauta gyara gasar domin kawo ɗauki ga matafiya da sauran al’umma.

“Ina kira ga Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa da ta gaggauta ɗaukar mataki kan wannan al’amari domin samar da mafita ga waɗannan ’yan kasuwa, kasancewar wannan hanya ita ce kaɗai take haɗe jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Neja da yankin Kudancin Najeriya.”

Ya bayyana cewa gadar, wadda ke Ƙaramar Hukumar Keɓɓe ta Jihar Sakkwato a kan hanyar zuwa Jihar Neja ita ce babbar mahaɗar yankin Arewa maso Yamma da yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.