Akalla gidaje 60 da kayayyaki na miliyoyin Nairori suka salwanta sakamakon wata ambaliya da ta mamaye Ƙananan Hukumomin Jihar Nasarawa guda biyu.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, Zachary Allumaga, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Lafiya, babban birnin Jihar ranar Asabar.
- Nigeria@63: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da safiyar Lahadi
- Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, ya fice daga PDP
Ya ce an samu ambaliyar ce a Kananan Hukumomin Lafiya da Toto a watan Agusta, kuma ta raba mutane da dama da muhallansu sannan dukiyoyi suka salwanta.
A cewar shugaban, a Lafiya, an samu ambaliyar ce a unguwar da galibi daliban Jami’ar Tarayya da ke Lafiya ne suke zama a cikinta.
Zachary ya ce ta lalata kwamfutoci da katifu da littattafai da kayan abinci da sauran kayayyaki.
A Karamar Hukumar Toto kuwa, ya ce ambaliyar ta lalata sama da gidaje 60.
Ya ce ambaliyar ta Toto ta samu ne sakamakon zaizayar kasa.
Shugaban ya ce tuni hukumar ta fata shirye-shiryen raba kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ta shafa.