✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, ya fice daga PDP

Sai dai bai bayyana inda ya koma ba a cikin wasikar

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, ya fice daga jam’iyyarsa ta PDP.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata wasika dauke da kwanan 30 ga watan Satumba dauke da sa hannun tsohon Gwamnan, wacce ya aike wa shugaban PDP na mazabar Ƙaura da ke Karamar Hukumar Zariya a Jihar.

Wasikar, mai taken “Takardar ficewa” ta ce, “Cikim godiya ga Allah maɗaukakim Sarki, na rubuto wannan takarda ne domin in yi gaisuwa a gare ka tare da sanar da kai kudurina barin jam’iyyar PDP.

“Sakamakon haka, na dawo da katina na shaidar zama dan jam’iyyar PDP daga ranar 30 ga watan Satumba 2023.

“A tare da wannan wasika, akwai katin nawa na shaidar zama ɗan jam’iyyar PDP wanda na hado dashi.”

Dr Mukhtar Ramalan Yero wanda har ila yau shi ne Dallatun Zazzau ya kasance tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kaduna lokacin Gwamna Patrick Yakowa wanda ya rasa rayuwar sa sakamakon hadarin jirgin sama.

Rasuwar Gwamna Yakowa ce ta ba shi dama daga bisa ni ya dare kujerar Gwamnan jihar Kaduna tun daga ranar 15 ga watan Disamba 2012 zuwa 29 ga watan Mayu 2015.

%d bloggers like this: