An tabbatar da mutuwar mutum tara sannan wasu bakwai sun bace a Seoul, babban birnin kasar Koriya ta Kudu, bayan mamakon ruwan sama na tsawon kwana uku.
Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tafka ruwan na tsawon kwana uku a jere ba kakkautawa.
- Tabarbarewar Tsaro: Gombe Ta Kafa Rundunar ‘Operation Hattara’
- Babu sunan Ahmad Lawan da Akpabio a ’yan takarar sanata —INEC
Sama da milimita 500 na ruwan sama ne ya sauka a birnin Seoul tun daga ranar Litinin har zuwa safiyar Laraba.
Ruwan ya sauka a yammacin birnin Incheon mai tashar jiragen ruwa, Lardin Gyeonggi, wanda ke kewaye da Seoul da lardin.
Ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar mutum tara da suka hada da biyar daga birnin Seoul, uku daga Gyeonggi da kuma daya daga Gangwon.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai dan kasar China, wanda ya mutu sakamakon zaftarewar kasa a birnin Hwaseong a daren ranar Talata, kamar yadda ofishin jakadancin China da ke Koriya ta Kudu ya bayyana.
Kimanin mutum 570 ne daga Seoul da Gyeonggi suka rasa matsugunansu, sai dai hukumomi sun kwashe mutum 1,253 daga yankin don tseratar da su.
Fiye da gidaje da gine-gine 2,600 ne ruwan ya shanye.