✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya ta ci mutum 3, wasu 50,000 sun rasa muhallansu a Kogi

Ba a taba garin irin wannan abin a 'yan shekarun nan ba.

Ambaliya ya yi ajalin wasu mutane uku ya kuma raba wasu 50,000 da matsuguninsu a Ibaji ta Jihar Kogi

Hakan ta faru ne sakamakon ambaliya da Kogin Neja da na Binuwai suka yi, a inda suka shafe karamar hukumar gaba dayanta.

Mai wakiltar Mazabar Ibaji a Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Honorabul Atule Egbunu ne ya tabbatar da hakan ga wakilinmu a hirar da ya yi da shi a Lakwaja a daren ranar Laraba.

Honorabul Egununu ya ce, “Ruwa ya shanye dubbban gonaki na jama’ar karamar hukumar, sannan kwashe mutanen yankin zuwa wani wuri ya gagara.”

Dan majalisar ya kuma ce, shi da al’ummar yankin ba su taba ganin musiba irin wannan ba.

Sannan ya yi kira ga gwamntin jihar da ta tarayya da kuma hukumomin agaji na ciki da wajen kasa da su kawo musu dauki.