✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Kananan hukumomin Yobe 5 na cikin hatsari

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta sake fitar da sabon gargadi ga yankunan da ke fuskantar babbar barazanar ambaliyar ruwa a Jihar…

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta sake fitar da sabon gargadi ga yankunan da ke fuskantar babbar barazanar ambaliyar ruwa a Jihar Yobe.

Yankunan da abin ya shafa inji hukumar sun ne Geidam, Bade, Bursari, Karasuwa, Yusufari da kuma Yunusari.

Babban Daraktan hukumar, Muhammad A. Muhammad shi ne ya fitar da gargadin a Damaturu babban birnin jihar yayin wata ziyarar wayar da kai da ya kai jihar.

Ya ce baya ga lalata gidaje da sauran dukiyoyi, matsalar ambaliyar da ke faruwa kusan a kowacce shekara a bana na barazana ga harkar samar da abinci.

Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin Dakta Abubakar Suleiman ya ce ko da yake matsalar sauyin yanayi na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ambaliyar, nauyi ne a kan gwamnatin jihar ta bullo da hanyoyin takaita aukuwarta a kowacce shekara.

Hanyoyin a cewarsa sun hada da bayar da gargadi da kuma ankarar da jama’a a kan lokaci kan barazanar, yin shirye-shirye a kan lokaci da kuma daukar matakan kariya.

Shugaban hukumar ta NEMA ya kuma ce hasashen ambaliyar na bana ya nuna cewa akalla kananan hukumomi 102 daga jihohi 28 ne ke fuskantar barazanar wacce tuni ta fara a barna sassa da dama na Najeriya.