Gwamnatin Jihar Borno ta ce za ta rufe duk sansanonin bayar da agaji 32 da aka kafa don tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri cikin makonni biyu, daga ranar Litinin da ta gabata.
Kwamishinan Yada Labarai, Farfesa Usman Tar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da manema labarai a Maiduguri ranar Laraba.
Ya ce ibtila’in ambaliyan ya raba kusan iyalai 30,000, da jimilla kusan mutane 600,000 d a gidajensu a fadin birnin.
“Gwamnatin jihar ta yanke shawarar cewa sansanonin ’yan gudun hijira ba za su ci gaba da aiki sama da makonni biyu ba.
“Muna tsammanin cewa ambaliyar ruwan za ta ragu sosai a cikin wannan lokacin, wanda zai ba mutane damar komawa gidajensu,” in ji Farfesa Tar.
Ya kuma yi gargadin cewa ci gaba da gudanar sansanonin zai kawo koma-baya ga nasarar da aka samu na rufe matsugunan ’yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa.
Farfesa Tar ya ce, “gwamnati ta kafa kwamiti don rarraba tsabar kudi da kayan abinci ga mutanen da suka rasa matsugunansu.
“Kowane mutum zai karɓi N10,000, buhun shinkafa 25kg, da kwalin taliya.
“Tuni dai rabon ya kai ga sama da kashi 40% na mazauna sansanonin, inda ake sa ran kammala aikin nan da ’yan kwanaki masu zuwa.”
Yayin da ake sa ran janyewar ruwan, Tar ya ce yawancin gidajen za su bushe kuma a shirye don masu su su zauna nan ba da jimawa ba.
“Ga waɗanda gidajensu suka lalace, gwamnati za ta samar da tantuna don matsuguni na wucin gadi har sai an fara aikin sake gina su.
“Bugu da ƙari, an tura ƙungiyar tantancewa ta gaggauta don tantance ɓarnar don yiwuwar bayar da tallafin kuɗi.
“Ma’aikatar noma tana ƙoƙarin kamo dabbobin da suka bace, ciki har da waɗanda aka samu a gidan namun dajin.
“Domin tabbatar da tsaro, an girke jami’an tsaro a wuraren da ruwa ya tsaya cak domin magance ayyukan ɓata-gari.”
Kwamishinan ya tabbatar da cewa, an samar da isassun sinadarai da za a rika hayaki da feahi domin magance gurbatar da kashe ƙwayoyin cuta a wuraren taruwar jama’a a fadin birnin.