Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko, amaryar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ta tare a dakinta a fadar sarkin a karshen mako.
Majiyar Aminiya da ta nemi a boye sunanta ta ce an daura auren Sarki Aminu Ado Bayero a kara auren ne a sirrance a ranar Juma’a a bisa sadaki Naira dubu 500.
- Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da kanwarsa a Kano
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Safarar Makamai A Zamfara
“An kai amarya dakinta da ke fada a ranar Asabar; an sanya daurin auren ne ba tare da an yayata ba; a kan haka Sarki ya gaggauta dawowa Najeriya daga ziyarar da ya kai kasar Maroko,” a cewar majiyar.
Rahotanni sun bayyana cewa amaryar ta fito ne daga zuriyar Malam Jamo, wanda dan uwa ne ga marigayi Sarkin Kano, Ibrahim Dabo.
An fara batun shirye-shiryen auren tsakanin Sarkin mai shekara 60 a duniya da kuma tsohuwar masoyiyarsa a shekarar da ta gabata.
An bayyana cewa sarkin ya kasance da mace daya sama da shekara 30 kuma suna da ’ya’ya hudu a tsakaninsu.
Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim, ne ya wakilci ango a matsayin waliyyi a wajen daurin auren, yayin da Alhaji Shehu Hashim, ya kasance waliyyin amarya.
Aminiya ta ruwaito cewa Makaman Bichi, Alhaji Isyaku Umar Tofa, Sarkin Dawaki Mai Tuta na cikin wadanda suka halarci daurin auren.