A wani lamari da za a kwatanta da biki mafi ban mamaki a cikin bukukuwan aure da aka yi a bana, wani dan kasar Indiya ya auri kanwar amaryar da ake shirin daura musu auri jim kadan bayan wadda zai aura ta samu bugun zuciya ta rasu a yayin bikin.
Lamarin da za a kwatanta shi da abu mai ban al’ajabi ya faru ne a makon jiya, a Gundumar Uttar Pradesh da ke Lardin Etawah na kasar Indiya.
Budurwar mai suna Surabhi da take dab da zama amarya, ba zato ba tsammani ta fadi a sume a kusa da angonta mai suna Manjesh Kumar, kafin fara addu’ar daurin aurensu ‘pheras,’ wadda muhimmiyar al’ada ce a bikin auren mabiya addinin Hindu a Indiya.
Bayanai sun ce ta fara rashin lafiya ne sai ta fadi wanda daga haka ya zama sanadiyyar ajalinta.
An kira motar daukar marasa lafiya, kuma duk da ma’aikatan lafiya sun yi iyakar kokarinsu don ceto ta a karshe sun tabbatar da rasuwar budurwar mai shirin zama amarya.
A yayin da mahalarta bikin suka yi zaton za a dage bikin saboda rasuwarta, amma hakan bai faru ba.
An ce dangin Manjesh da Surabhi sun zauna sun tattauna hanyoyin da za a bi, kuma a lokacin ne wani daga cikinsu ya ba da shawarar cewa, angon ya auri kanwar marigayiyar mai suna Nisha inda iyayen amaryar suka amince.
“Ba mu san abin da za mu yi a halin da ake ciki ba. Duk dangi sun zauna tare, kuma wani ya ba da shawarar cewa a aurar da kanwar wacce ta rasu mai suna Nisha ga angon.
“Iyalan bangarorin biyu sun tattauna batun kuma dukkansu sun amince,” kamar yadda dan uwan Surabhi mai suna Saurabh ya bayyana.
Ya kara da cewa, “Wani yanayi ne mai ban mamaki yayin da ake yin bikin kanwar wacce ke shirin zama amarya inda aka ajiye gawar ’yar uwata kwance a wani daki.”
Kamar yadda za ku iya tunani, an gudanar da bikin auren a cikin wani yanayi na matukar damuwa, saboda gawar Surabhi na cikin dakin da ke kusa da wajen da ake sha’anin bikin.
Nisha ta yarda da auren saurayin yayarta ce domin bin umarnin iyayenta.
“Wannan kira ne mai wahala ga danginmu. Gawar ’yar uwarmu da ta rasu tana daki, yayin da ake daura auren wata ’yarmu a wani daki a kusa. Ba mu taba ganin irin wannan fargaba ba.
Bakin cikin rasuwarta da kuma farin cikin bikin, har yanzu bai gushe ba,” inji kawun Surabhi mai suna Ajab Singh.