’Yan sanda sun tsare wata amarya kan zargin ba wa angonta guba ta kashe shi bayan mako biyu da ɗaurin aurensu a Jihar Kano.
Ana zargin amaryar ta kashe ango nata ne ta hanyar sanya masa maganin ɓera ne a cikin abincinsa.
Amaryar ta aikata wannan ɗanyen aiki ne a unguwar Yakasai da ke birnin Kano a ranar Alhamis na makon da ya gabata.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Haruna Kiyawa ya ce an garzaya da angon mai suna Umar Sani zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano inda a nan ne rai ya yi halinsa.
- Ango ya zargi amarya da zuba guba a abincin baƙi a Jigawa
- Ɗan Sanda cikin maye ya saki masu laifi 13 don murnar sabuwar shekara
Kiyawa ya ce ya ce dangin ango me suka kai wa ’yan sanda ƙara a ranar Litinin, bayan faruwar lamarin.
Ya ce ko da ’yan sanda suka je gidan, amaryar ta riga ta cika bujenta da iska, amma daga bisani an yi nasarar kamata a ranar Laraba.
Jami’in dan sandan ya ce a halin yanzu tana tsare tana amsa tambayoyi a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar kafin a gurfanar da ita a gaban kotu.