Kotun Majistare ta Wudil da ke Jihar ta yanke hukuncin daurin wata hudu ko zabin biyan tarar Naira dubu 20 da kuma biyan diyyar Naira dubu 200 ga wata amarya mai suna A’isha Lawan da kotun ta samu da laifin karya kugu da hannun uwangidanta mai suna Safiya Muhammad lokacin da suka yi takaddama kan rabon kwanan aure a tsakaninsu.
Alkalin Kotun Mai shari’a Kabiru Sallau ne ya yanke hukuncin bayan da wadda ake zargin ta amsa laifinta tare da gabatar da shaidu kan tuhumar da ake yi mata, sai dai alkalin ya ce amaryar za ta iya biyan kudin diyyar ga uwargidan tata daki-daki ba dole sai ta biya a dunkule ba.
Tun farko a takardar karar da ’yan sanda suka gabatar ga kotun sun ce amarya A’isha ta yi takkakkiya ce har gidan uwargidan bisa zargin ta tauye mata kwananta na aure inda ta zargi uwargidan da hana mijinsu ya je gidanta. Takardar ta ce “Bayan amaryar ta je gidan uwargidan ne sai suka shiga musayar magana inda a karshe uwargidan ta ce ita ce ta hana mijinsu ya je gidan amaryar. Nan take A’isha ta dauko wata tabarya da ke ajiye a gidan ta sauke ta a kan kugun uwargidan sannan ta kara dagawa ta rafka mata a hannu inda hannu da kugun nata suka karye.”
Duk da cewa wacce ake zargin ta amsa laifinta amma ta ce a lisafinta kwanan aurenta ne mijin ya dauka ya kai wa uwargida don haka ta je gidan don neman hakkinta. Kuma a cewarta ba ta yi tsamamnin dukan da ta yi wa uwargidan zai zama sanadin raunata ta ba, don haka ta nemi sassaucin kotu a kan hukuncin da za ta yanke mata.
Lokacin da Alkalin Kotun Mai shari’a Kabiru Sallau ya nemi ganin uwargida an shaida masa cewa tana can a kwance ba ta ma san wanda ke kanta ba saboda raunukan da ta samu, sai dai lauyanta ya nemi kotu ta tilasta amaryar ta biya diyyar Naira dubu 500 na maganin da ake yi wa uwargidan.
Da yake bayar da shaida mijin matan, mai suna Zaharadden Yusuf ya ce “Abin da ya faru uwargidan ba ta dade da komowa gidan ba, don haka da na je gidanta sai na yi kwana biyu. Lokacin da amaryar ta nemi bayani a kan cewa ai ranar girkinta ne sai na yi mata bayani cewa na mayar da kwanakin auren nasu zuwa kwana bibbiyu don haka na ba ta hakuri don ta tafi gida inda na gaya mata cewa kwana bibbiyun ba abu ne na damuwa ba. Bayan na koma daki ne ban yi aune ba sai jin ihun uwargidan, ko da na fito sai na tarar cewa tuni mai faruwa ta riga ta faru.”
Bayan jin ta bakin bangarorin ne Mai shari’a Kabiru Sallau ya daure amaryar wata hudu a kurkuku ko ta biya tarar Naira dubu 20, kuma ya ce ta biya diyyar Naira dubu 200 ga uwargidan don yi mata magani.