Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jos, babban birnin Jihar Filato ta aike da tsohuwar Ministar Ruwa, Sarah Ochekpe, zuwa gidan gyaran hali.
Kotun ta kuma aike da karin wasu karin mutum biyu; Raymond Dabo da Evangelist Leo Sunday Jitung hukuncin daurin wata uku kowannensu.
- Dalilin da ya sa China ta daina ba Najeriya bashi – Lai Mohammed
- Dalibin da ake zargi da kwakule wa budurwarsa idanu ya zama ‘kurma’ rana tsaka a kotu
Mutane ukun dai na fuskantar tuhume-tuhume ne tsawon shekara hudu kan zargin hada baki don yin almundahanar wasu kudade.
Sai dai kotun ta bayar da zabin biyan tarar Naira miliyan daya ga kowannensu.