✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Almajiri ya kashe almajirin da ke qoqarin sulhunta su

Ana zargin wani almajiri mai suna Babangida Abubakar mai shekara 20 da kashe xan uwansa almajiri mai suna Mansur Ibrahim ta hanyar farke masa wuya…

Ana zargin wani almajiri mai suna Babangida Abubakar mai shekara 20 da kashe xan uwansa almajiri mai suna Mansur Ibrahim ta hanyar farke masa wuya da wuqa a ranar Litinin xin makon jiya lokacin da marigayin yake qoqarin sulhunta su a kan taqaddamar bashi.

Lamarin ya faru ne da misalin qarfe tara na dare lokacin da Babangida Abubakar wanda aka kawo shi almajiranci daga garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, ya kashe Mansur Ibrahim mai shekera 23 wanda shi kuma aka kawo shi almajiranci daga garin Jangargari da ke Jihar Neja.

Wakilin Aminiya ya ziyarci Rimin Danza, Unguwar Iya, Zariya inda lamarin ya faru, inda  ya tarar da ana qoqarin yin jana’izar marigayin, kuma malamin marigayin mai suna Alaramma Malam Isa wanda aka fi sani da Alaramma Isa Mai Babban Allo, ya yi masa bayani kamar haka. “A gaskiya muna cikin alhini domin kusan abin ya faru ne a tsakanin maqwabta domin malamin almajirin da ya kashe min almajiri aminina ne kuma koyaushe muna tare, kuma duk ana unguwa xaya. Yadda na samu labari shi ne almajirina ya je ne domin ya yi sulhu a tsakanin qanensa da wanda ya yi kisan, saboda qanen marigayin yana bin wancan bashin kuxi, amma ya qi biyan sa, to sai suna jayayya shi marigayin ya je domin shiga tsakani. Sai shi Babangida da ake bi bashi ya zaro wuqa ya farqe masa maqogoro inda nan take Mansur ya faxi, kafin in isa wurin an kwashe shi zuwa asibiti, sai na bi su, ina isa da na ga irin yakan da aka yi wa Mansur da halin da yake ciki da irin jinin da yake zuba na san zai yi wuya ya rayu,” inji malamin.

Ya qara da cewa: “Kafin wani lokaci Allah Ya yi masa cikawa kuma dama an sanar da ’yan sanda shi kuma wanda ya aikata kisan ya tsere.  Bayan nan sai ’yan sanda suka ba mu dama cewa mu yi masa sutura, har iyayen marigayin sun iso daga can Neja, haka su ma iyayen wanda ya yi kisan sun zo daga Saminaka duk muna tare da su. Kuma kamar yadda ka gani muna shirin yi masa jana’iza ce. Kusan shekarata 45 ina koyar da almajirai karatun allo, saboda wajen mahaifina na gada, amma ba mu tava ganin irin wannan tashin hankali ba, a ce almajiri ya kashe xan uwansa almajiri, sai wannan karo.”

Aminiya ta tuntuvi malamin Babangida Abubakar da ake zargi da kisan mai suna Alaramma Muhammadu Kabiru inda ya ce, “Ana ta cewa wai ni ne malaminsa, ni ba malaminsa ba ne, kuma ban san shi ba, ban tava ganinsa ba, domin da ya zo ba a kawo shi gabana ba, kuma ban san ko daga ina ya zo ba. Don haka ba almajirina ba ne, kuma ina da tsari a kan almajiraina, kullum ina yi musu gargaxin cewa kada su kuskura su yi faxa da kowa, idan wani ya tone su, to kada su kula shi su kawo shi qara wurina zan xauki matakin da ya dace, don haka almajiraina ba sa faxa da kowa don haka ba ruwana.”

Shi kuma mahaifin marigayi Malam Ibrahim wanda ya halarci jana’izar xansa cewa ya yi, “Abin da zan faxi shi ne Allah Ya jiqan Mansur da ni da mahaifiyarsa duk mun yafe masa, kuma Allah Ya jiqansa,” sai ya fashe da kuka.

DPO Kasim Abdul, Babban Jami’i a Ofishin ’Yan sanda na Qofar Fada, Zariya ya tabbatar da faruwa lamarin, ya ce a lokacin suna shirin yi jana’izar almajirin ne, kuma zai zauna da malaman almajiran da iyayen yaran domin nanata muhimmancin zaman lafiya da juna.

Daga baya ya shaida wa wakilinmu cewa sun samu nasarar kama wanda ake zargi da kisan, kuma sun tura shi hedkwatarsu da ke Kaduna domin ci gaba da gudanar da bincike.