✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Almajiranci irin na Kirista (9)

Wane ne almajiri? Har yanzu muna koyarwa ne a kan ko wane ne almajiri? Mun ga yadda mutum zai iya shiga cikin irin wannan horarwa;…

Wane ne almajiri?

Har yanzu muna koyarwa ne a kan ko wane ne almajiri? Mun ga yadda mutum zai iya shiga cikin irin wannan horarwa; wato ta wurin ba da gaskiya ga Yesu Kiristi a matsayin shi ne kadai mai ceton duniya; idan ba ta wurin Yesu Kiristi ba, babu begen samun rai na har abada. Dole ne idan muna so mu samu rai na har abada bayan mun mutu cikin wannan duniya, hanyar daya ce kawai: Yesu Kiristi da kansa ya koya mana cewa: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne Rai, ba mai zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14: 6).
Abu na biye shi ne kamar yadda maganar ke fadi a cikin Littafin Matta 11: 28 – 30: tana cewa, “Ku zo gare ni dukanku ku da kuke wahala, masu nauyin kaya, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku dauka wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina, gama ni mai tawali’u ne, mai kaskantar zuciya, za ku samu hutawa ga rayukanku, gama karkiyata mai sauki ce, kayana kuma marar nauyi.” Daga wannan wurin da muka yi karatu; za mu gane cewa: almajiri; shi ne wanda ya yarda ya dauka wa kansa karkiyar Yesu Kiristi.
Ku dauka wa kanku karkiyata: Wannan abu ne wanda mutum yake yi da yardar ransa, babu tilas a ciki, sai dai idan har mutum yana so ya dauki kamanin Yesu Kiristi cikin rayuwarsa ta yau da kullum, to babu wata hanya sai mun yarda mun yanke shawara cewa za mu dauki karkiyar Yesu Kiristi a wuyanmu; ba tilas ba amma da yardarmu ne, mun yarda mun ba kanmu shawara mu shigo cikin wannan dangantaka ta almajiranci. Mu sani fa cewa, dalilin zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya dole ne ya zama dalilin rayuwa na almajiransa. Almajiri ba ya da wani aiki daban da na ubangijinsa, aikin da ubangiji Yesu yake yi, shi ne aikin da almajirinsa zai ba da kansa muddar ransa kuma har abada. Ko kai malamin makaranta ne, ko kuwa kai likita ne, ko kai alkali ne, ko mene ne sana’arka, dalilinka na rayuwa ya zama dalilin zuwan Yesu Kiristi cikin duniya.Yesu Kiristi ya yi alkawarin ba da hutu ga kowane mutum da ke wahala, masu nauyin kaya; mu sani fa kayan zunubi yana da nauyi ainun. A cikin aya ta 29, Yesu Kiristi ya yi wannan magana ya ce: “Ku dauka wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina, gama ni mai tawali’u ne, mai kaskantar zuciya: za ku samu hutawa ga rayukanku.”
Ina so mu gane wani abu sosai daga wurin da muka yi karatu; akwai bambamci kadan tsakanin hutawa da Yesu ya ambata a aya ta 28 da hutawar da ya ambata a aya ta 29, yayin da kowane mutum zai samu hutu daga ikon zunubi da Shaidan ta wurin gafarar zunubansa; zai kuma samu hutu daga kangin rashin lafiya da mai yiwuwa kalubalen aljani, biye da wannan irin hutun kuma akwai hutun da mutum zai samu ta wurin kawo kansa cikin cikin horarwa ta almajiranci, wannan ba dole ba ne. Kamar yadda mutum ya amsa kiran Yesu Almasihu domin ya zama mai cetonsa, haka nan ya kamata ka amsa wannan kira na zama almajiri. Babu tilas a ciki. Sa’add Yesu Kiristi ya ce ku zo gare ni, bai ce ku zo wurina a dole ba ko kadan; sai kuma ya dada cewa ku dauka wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina… idan har kana bukatar samun hutu wa ranka, to kana bukatar amsa wannan gayyata ta dauka wa kanka karkiyar Yesu Almasihu da kuma yin koyi da rayuwarsa. Babu wata hanya daban da wannan da zarar mun samu ceto daga rayuwar zunubi, babu shakka za mu samu hutu daga kuncin zunubi, amma bai kamata mu tsaya a wurin kawai ba, muna cewa mun samu hutu daga bautar zunubi. Eh, yana da kyau mun samu ceto, to sai mu kawo wuyanmu karkashin karkiyar Yesu Kiristi ta wurin yardar ranmu domin koyo daga wurinsa; har sai mun kamantu da shi Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Akwai masu bi da dama wadanda suke ganin cewa, da yake sun rigaya sun samu ceto; babu sauran abin da ya rage musu su yi, wadansu suna ganin suna iya yin wani hidima cikin ekklisiyar Almasihu, a ganinsu sun rigaya sun kure, amma gaskiyar ita ce, idan har mutum ya samu wata albarka daga sama, ya kuma sadu da Allah ta wurin ban-gaskiya cikin Yesu Kiristi, amma bai taba daukar mataki na zaman almajirin Yesu Kiristi ba; babu shakka duk abin da yake tsammani yana da shi ; zai ga cewa ba da jimawa ba zai yankwane ya kuma lalace a hannunsa. Akwai baye-baye da dama da masu bi za su iya bayyanawa, amma idan ba su iya kawo kansu karkashin karkiyar Yesu Kiristi domin su yi koyi da rayuwarsa ba, to babu shakka za su karasa a cikin Jahannama na har abada.
Almajirai ne kadai da ake kamantasu da siffar Ubangijinmu Yesu Kiristi, ke da ikon shiga mulkin sama, domin suna da Rai na har abada. karkiya dai ita ce itacen da ake sawa bisa wuyan shanu biyu domin su ja garmar noma da ita; karkiya ba za ta barka ka yi abin da ka ga dama ba, karkiya takan tilasta maka ka yi tafiya daidai da wanda karkiyar ta hada ku tare da shi. Wannan ne ya sa lokacin da Yesu Kiristi ya yi magana ya ce: “Ku dauka wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina….” Yana nufin cewa, ka ba ni sunanka, domin duk inda na tafi, can kai ma za ka tafi; abin da na sa hannu a ciki, shi ne za ka ci ko za ka sha, duk wanda ya yi wannan da yardar rai, shi almajirin Yesu Kiristi ne. Akwai babbar damuwa idan mutum ya kasance karkashin wata karkiya, sai kuma ya ce zai kawo kansa karkashin wata karkiya ba tare da ya zare wuyansa daga wancan karkiya ta farko ba, babu yadda zai iya bi; domin muyanka daya ne kawai, ba zai iya daukar karkiya biyu a lokaci guda ba; ba za ka iya bauta wa iyayengiji biyu ba a lokaci daya, ba ya yiwuwa. Idan har yanzu kana karkashin azaba ta zunubi, ko azabar Iblis, dole ne ka/ki/su/ koma ga bauta wa Allah Shi kadai; ka manne wa Yesu Kiristi shi kadai. Hanyar jin dadin shi ne mutum ya kawo kansa karkashin karkiya daya tak, wato ka bar daukar sauran karkiya; ka kawo wuyanka da yardar ranka karkashin karkiyar Ubangiji Yesu Kiristi. Mu sani fa cewa Ubangiji Yesu Kiristi yana shirye a koyaushe ya hada karkiya da kai kuma ya maishe ka abin da kake so ka zama.
Mu shigo cikin makon zabe, sai mu nemi nufin Allah cikin addu’a domin mu zabi nagari. Bari Allah Ya sa a yi zabe cikin lumana, Ubangiji Allah kuma Ya ba mu salamarSa, amin.