✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Almajiranci irin na Kirista (5)

Ina so a yau mu kammala koyarwarmu a kan mene ne almajiranci; kafin mu shiga bincike a kan ko wane ne almajiri. Almajiranci ba abu…

Ina so a yau mu kammala koyarwarmu a kan mene ne almajiranci; kafin mu shiga bincike a kan ko wane ne almajiri.

Almajiranci ba abu mara fasali ba ne. Yana nan bi-da-bi, daya bisa daya: A cikin Littafin Ishaya 28: 9-10, maganar Allah na cewa “Wannan dai za ya koya wa wane ne sani? Za shi bayyana wa wane ne jawabin, shi gane? Wadanda aka yaye su daga nono, aka cire su daga mama? Gama, umarni a kan umarni, ka’ida a kan ka’ida, ka’ida a kan ka’ida; nan kadan can kadan.” Haka nan kuma cikin Littafin Misalai 16:9, maganar Allah tana cewa “Zuciyar mutum takan shawarci hanyarsa: amma Ubangiji yana nuna masa wurin takawa.” Ainihin shirin almajiranci daga wurin Allah ne; bisa ga umarnin da ya bayar, akwai hanyar horarwa daban-daban, haka nan kuma bisa ga lokuta da shi Ubangiji ya shirya cikin nufinsa. A karshe cikin wannan sashi, ina so mu gane tun daga nan cewa, akwai sharudda da ke tafe da almajiranci, ina so mu san wannan sosai – cikin Littafin Luka 9:23 maganar Allah na cewa “Ya ce musu duka, idan kowane mutum yana nufi ya bi ni, sai ya yi musun kansa, ya dauki gicicyensa kowace rana, ya biyo ni.” Bari mu duba wani misali da Yesu Kiristi ya bayar a cikin Littafin Luka 14: 25 – 33 “Taro mai yawa suka tafi tare da shi: ya waiwaya ya ce musu; Idan kowa ya zo wurina, ba ya ki ubansa da uwatasa da matatasa da ’ya’yansa da ’yan uwansa maza da mata ba, i, har da ransa kuma, ba shi da iko shi zama mai bina ba. Dukkan wanda bai dauki giciye na kansa ba, ya zo bayana, ba ya da iko ya zama mai bina ba. Gama wane ne a cikinku idan yana so ya gina soro, ba yakan fara zaunawa tukuna ya yi lissafin tamanin gini, ko yana da abin da za ya gama shi ba? Kada ya zama, sa’anda ya rigaya ya sa tushe, ya kasa gamawa sai dukkan masu duba su yi ta yi masa ba’a, su ce, wannan mutum ya soma gini, ya kasa gamawa. Ko kuwa mani sarki ke nan, da za ya gamu da wani sarki a yaki, ba za ya zauna ba tukuna ya yi shawara, ko shi da mutum zambar goma, ya iya karo da wanda yake kawo masa yaki da zambar ashirin? In ba ya iya ba, tun wancan yana da nisa kwarai tukuna, shi aike Manzanni su tambayi shirin amana. Haka nan fa kowane ne da ke cikinku da ba ya rabu da dukan abin da ke nasa ba, ba shi da iko shi zama mai bi na.”
Da zarar Yesu Kiristi ya yi wannan magana, mutane da yawa daga cikin wadanda suke bin sa suka juya suna cewa wannan abin akwai shi da wahala.; duka da haka Yesu Kiristi bai sassauta wadannan sharuddan ba: wani saurayi basarauce ya tafi da bakin ciki da aka fuskance shi da sharuddan bin Yesu Kiristi, kuma Ubangijinmu Yesu Kiristi bai bi shi da gudu ba. “Sa’anda yana fita zuwa kan hanya wani ya sheko masa a guje, ya durkusa a gabansa ya tambaye shi, Malam managarci, me zan yi domin in gaji rai na har abada? Yesu ya ce masa, don me kake ce da ni managarci? Babu wani managarci sai daya, Allah. Ka san dokokin, ba za ka yi kisan kai ba, Ba za ka yi zina ba, ba za ka yi sata ba, ba za ka yi shaidar zur ba, ba za ka yi zalunci ba, ka bada girma ga ubanka da uwarka, ya ce masa, Malam, na kiyaye wadannan tun ina saurayi. Yesu da dubansa ya kaunace shi, ya ce masa, Abu daya ka rasa: ka tafi, ka sayar da abin da kake da shi duka, ka ba fakirai, za ka samu wadata a sama: ka zo kuma, ka biyo ni. Amma gabansa ya fadi saboda wannan batu; ya tafi yana bakin ciki; gama mai arziki ne shi ainun. Yesu ya dudduba kewaye da shi, ya ce wa almajiransa, Da kyar masu dukiya za su shiga cikin mulkin Allah. Almajiran suka yi mamaki saboda zancensa, Amma Yesu ya sake amsawa, ya ce musu, ’Ya’yana, da kyar kamar me masu dogara da dukiya za su shiga cikin mulkin Allah. Da mawadaci ya shiga cikin mulkin Allah, ya fi sauki rakumi ta shiga ta kafar allura. Suka yi mamaki gaba da misali, suka ce masa, wane ne fa za shi tsira? Yesu ya dube su, ya ce, a wurin mutane ba shi yiwuwa, amma ga Allah ba haka ba, gama ga Allah abu duka ya yiwu. Bitrus ya soma ce masa, ga mu mun bar abu duka mun bi ka. Yesu ya ce, Gaskiya ina ce muku, ba mutum wanda ya bar gida, ko ’yan uwa maza, ko ’yan uwa mata, ko uwa, ko uba, ko ’ya’ya, ko gonaki, saboda ni da bishara, da ba za ya karbi ribanya dari yanzu cikin wannan zamani, gidaje da ’ya uwa maza da ’yan uwa mata da uwaye da ’ya’ya da gonaki, game da tsanani; a cikin zamani mai zuwa kuma rai na har abada. Amma da yawa da ke na farko za su zama na karshe, na karshe kuma za su zama na farko.” (Markus 10: 17 – 31).
Gaskiyar shi ne idan mutum bai gane wadannan sharudda ba, ba zai iya zama cikakken almajirin Yesu Kiristi ba. Za mu kara bayani sosai kan wadannan sharudda
Almajirtarwa shi ne babban umarnin da Yesu Kiristi ya bar wa masu bin sa. Wannan shi ne babban abin da yake kan kowane mai bin Yesu. Abin da Allah ya sa rai cewa zai faru da duk wanda ya zo gare shi, shi ne, ya dauki kamaninsa; sharuddan da ya ba wa masu bin sa a da shi ne sharuddan har yau, bai canja ba kuma ba zai taba canjawa ba. Babu yadda za mu samu masu bin Yesu na gaskiya idan ba mu almajirtar da su ba, shi ya sa dole mu mai da hankali kan renon almajirai har sai sun girma.
Idan Allah ya yarda za mu soma bincike a kan WANE NE ALMAJIRI! Sai mu ci gaba da yin addu’a domin Allah ya ba mu zaman lafiya cikin wannan kasa; musamman ma a lokacin wannan zabe na kasa.
Allah ya taimake mu duka, amin.