Har yanzu dai muna kan bayyana ko mene ne almajiranci; makon da ya shige mun tsaya ne a kan cewa almajiranci hanyar kamantuwa ne da surarsa, kuma wannan ba zai taba faruwa ta wurin ganawa da shi sau daya kawai ba, dole ne a bi shiryayyun matakai, koyarwa da horarwa da aka shirya a hankali har sai nufin Allah Ya cika. A yau; za mu ci gaba ne da yin bincike har sai mun kai ga cikakken ganewa na ko mene ne almajiranci.
Almajiranci ya kunshi ganawa da kuma cudanya da Ubangiji da kanSa a cikin addu’a, cikin kalmarSa, haka cikin yin hidima da bin sawayenSa ko gurbinSa. A cikin Littafin Yohanna 8:31–32 , maganar Allah na koya mana daga bakin Yesu Kiristi da kansa cewa: “Yesu fa ya ce ma wadannan Yahudawa da suka ba da gaskiya gare shi, idan kun zauna a cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske; ku san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantar da ku.” Abin da yakan biyo bayan ba da gaskiya ga Yesu Kiristi, shi ne zama cikin maganarsa, wato yin nazari da kuma yin biyayya ga abin da muka koya. Akwai bambamci tsakanin sanin abin da maganar Allah ke fadi da kuma aikata abin da Allah Ya fadi, sani ba aikatawa abu ne mara amfani ga kowane mai bin Yesu Kiristi, kiran da muke da shi, shi ne na bin gurbin Yesu Kiristi Ubangijinmu. A cikin Littafin 1Bitrus 2: 21, maganar Allah na koya mana cewa: “Gama zuwa wannan aka kiraye ku; Kiristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar muku gurbi, domin ku bi sawunsa.” Dole mu gane wannan idan har za mu zama almajirai na kwarai – bin gurbin da ya bar mana; shi ne ya sa yau; Ubangiji yana neman mutane maza da mata a tsakaninmu wadanda za su zama abin koyi ga masu bi domin su fahimci irin rayuwar da ake bukata su yi. Zama almajirin Yesu Kiristi ba shi yiwuwa da baki kawai, dole mu zauna tare da shi cikin maganarsa da kuma lura da rayuwar wadanda suka gane wannan irin rayuwar kuma suna rayuwarsu kamar yadda shi Ubangijinmu yake so.
Almajiranci, ga kowane mutum, abu ne na musamman ga shi mutumin; abin nufi a nan shi ne, shirye-shiryen darussa da hanyar ganawa da Ubangiji da irin kayan aikin da za a nema da kuma ko yaya saurin wannan koyarwa zai kasance, ya bambanta daga wani zuwa wani, ba lallai ba ne duka mu zama bai-daya; hanyar da kowane mutum zai bi zuwa daukaka ta bambanta da ta wani: wannan shi ya sa ba za mu iya kwatanta kanmu da wani ba cikin cudanyar da muke yi da shi Almasihu. Kowane dayanmu Allah Ya ba mu namu sashi na aikin da ya kamata mu yi; ga shi wanda aka bayar da yawa daga wurinsa za a bidi mai yawa. Bari mu dauki misali daga cikin Littafin Yohanna 21: 15 – 25 da ke cewa “Sa’anda fa suka karya kumallonsu, Yesu ya ce ma Simon Bitrus dan Yohanna, ka fi wannan kauna ta? Ya ce masa, I Ubangiji; ka sani ina sonka. Ya ce masa, ka yi kiwon ’ya’yan tumakina. Ya sake fadi na biyu, Simon dan Yohanna, kana kauna ta? Ya ce masa, I Ubangiji, ka sani ina sonka. Ya ce masa, ka zama makiyayin tumakina. Ya ce masa har na uku, Simon dan Yohanna, kana sona? Zuciyar Bitrus ta baci sabada fadin nan na uku da ya yi masa, kana sona? Ya ce masa fa, Ubangiji, ka san abu duka: ka sani ina sonka. Yesu ya ce masa, ka yi kiwon ’yan tumakina. Hakika, hakika ina ce maka, sa’anda kana yaro, kakan yi damarar kanka, kakan yi yawo inda ka nufa: amma sa’anda ka tsufa, za ka mika hannuwanka, wani zai yi maka damara, zai kai ka in da ba ka so ba.Ya fadi wannan yana kwatanta irin mutuwa da zai girmama Allah da ita. Sa’anda ya fadi wannan fa, ya ce masa, ka biyo ni. Bitrus ya waiwaya, ya ga almajirin nan da Yesu yana kauna tasa yana bi, shi wanda yana jingina ga kirjinsa wurin cin abinci, wanda ya ce kuma, Ubangiji, wane ne shi wanda yana bashe ka? Bitrus fa, da ya gan shi, ya ce ma Yesu, Ubangiji, wannan mutum fa, me za ya yi? Yesu ya ce masa, idan ina so shi zauna har na zo, ina ruwanka? Kai dai ka biyo ni. Wannan batu fa ya tafi wurin ’yan uwan, wai, wannan almajiri ba za ya mutu ba: amma Yesu ba ya ce masa ba za ya mutu ba: amma idan ina so, shi zauna har na zo, ina ruwanka? Shi ne wannan almajiri wanda yake shaidar wadannan al’amura, ya kuma rubuta wadannan abu: mun sani kuma shaida tasa gaskiya ce. Akwai kuma wadansu abu da yawa da Yesu ya yi; ina tsammani da za a ce za a rubuta su kowane daya da duniya da kanta ba za ta dauki littattafai wadanda za a rubuta ba.”
Yesu Kiristi yana faman ba wa Bitrus aikin da zai yi; shi kuwa Bitrus yana kokarin tuna wa Yesu cewa yaya kamar shi kadai ne kawai ake ba wa aiki, kuma ga daya daga cikin almajiran da kamar Yesu Kiristi bai damu da ba su wani aiki ba. Kowane dayanmu yana da ainihin aikin da Allah Yana so mu yi. Wannan aiki kuwa ya shafi kowane fannin rayuwarmu na yau da kullum. Yesu Kiristi ya yi wani kwatance cikin Littafin Matta 20:1– 6; 14 – 15, yana cewa, “Gama mulkin sama yana kama da shi ke ubangida, wanda ya fita tunda sassafe garin ya yi ijara da ma’aikata su zo gonarsa. Sa’anda ya shirya da ma’aikata a kan sule- sule kowace rana, ya aike su cikin gonarsa. Wajen sa’a ta uku ga yini ya fita kuma, ya ga wadansu suna tsaye banza cikin kasuwa; ga wadannan kuma ya ce, ku kuma ku tafi cikin gona, iyakar abin da ya wajaba, na ba ku, Suka kama hanya. Ya sake fita wajen sa’a ta shida da sa’a ta tara ga yini kuma, ya yi irin na da. Wajen sa’a ta goma sha daya ga yini kuma ya fita, ya iske wadansu a tsaye; ya ce musu, don me kuke yini a nan tsaye banza? Suka ce masa, don babu wanda ya yi ijara da mu. Ya ce musu ku kuma ku tafi cikin gona……..dauki abin da ke naka, ka yi tafiyarka; nufina ne in ba na karshen nan daidai da kai. Ba halal ne ba a gare ni in yi abin da na nufa da abina? ….”. Almajiranci; damka rayuwarmu ne cikin hannun Ubangiji, Allah Ya yi da mu yadda ya gani ya dace, mu kuma mu iya mika kanmu gare shi cikin biyayya musamman ga maganarsa.
’Yan uwana, mu ci gaba da yin addu’a domin wannan kasa Najeriya, musamman ma domin zaben da ake shirin yi nan gaba. Ubangij Allah Ya ba mu zaman lafiya, amin.