✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Yana kin Wanda Ba Ya RokonSa

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa ranar karshe. 

Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alkhairin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam. Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, yau mukalarmu za ta gudana ne a kan jan hankali zuwa ga rokon Allah, lamarin da Shi Allah Yake fushi da duk wanda yake bijire masa, yana yin girman kai dangane da shi. Lallai dan Adam da yawa akan sami wadanda ba su son a roke su komai, ko kuma da yawa idan an roke su sun bayar, sukan yi fushi idan an yawaita rokon nasu, har ma su ji ba sa son wanda yake rokon. Allah, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, a matsayinSa na Wanda wani abu bai yi kama da Shi ba, alhalin Yana ji, Yana gani, fushi Yake da wanda ba Ya rokonSa.
Alkur’ani, wanda shi ne farkon kundin da za a duba dangane da duk wata mas’ala ta rayuwar Musulmi, ya yi magana bayyananna dangane da wannan al’amari da kin rokon Allah, kamar yadda ya zo a cikin Sura ta 40 (Ghaafir), aya ta 60. Allah Yana cewa, “Kuma Ubangijinku Ya ce, ‘Ku kira (roke) Ni in karba muku. Lallai wadannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama suna kaskantattu.”
Bayani ya zo a cikin tafsirin Ibnu Katheer cewa, “Allah Ya ba mu karsashin mu roke Shi, kuma Ya ba mu tabbacin Zai karba mana addu’armu.” Ke nan wannan kira, shi ne addu’ar da ake magana game da yin ta, kuma ita ce aka bayyana ta a matsayin bauta, kamar dai yadda wani hadisi ingantacce ya nuna: An samo daga Nu’uman dan Bashir, Allah Ya yarda da su, ya ce, Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Addu’a ita ce ibadah. Sannan sai ya karanta ayar da ta gabata, wato Sura ta 40, aya ta 60.” Imam Ahmad da Haakim suka ruwaito shi, kuma Shaikh Nasiruddinil Albaniy ya inganta shi a cikin littafin Sahihul Jami’u, hadisi na 3,407.
A cikin tafsirin Ibnu Katheer din ne dai aka nuna cewa, wani daga cikin magabata, Sufyan Atthauriy yakan ce, “Ya Wanda Ya fi son duk wanda yake rokonKa; Ya Wanda Ya fi kin duk wanda ya ki ko ya yi girman kai wajen rokonKa; Kuma lallai babu wani kamar Kai a wannan siffa!” Ibnu Abiy Haatim ne ya ruwaito wannan.
Haka nan wani mai wake yana cewa, “Allah ba Ya kin a roke Shi, amma dan Adam (shi ne) yake kin jinin a roke shi.” Imamul katadah ya ce, “Ka’abal Ahbaar ya ce, ‘An ba wannan al’umma (Musulmi) abubuwa uku da ba a ba kowace al’umma gabaninta ba, sai dai Annabawa: (1) Idan Allah Ya yi aike ga wani Manzo, sai Ya ce masa, ‘Kai shaida ne ga al’ummarka’, su kuwa musulmi (al’ummar Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam), sai aka ce su ne shaida kan dukkan al’ummomin da ke gabaninsu; (2) Allah na fada wa kowane manzo cewa, ba a dora masa wahala a cikin addini ba; su kuwa musulmi, sai Allah Ya ce musu (gaba daya), kamar yadda ya zo a cikin Sura ta 22 (Suratul Hajji), aya ta 78, “…Shi ne Ya zabe ku, alhali kuwa Bai sanya wani kunci ba a kanku a cikin addini.”
A karkashin wannan ne ma Shaikh Abubakar Mahmud Gumi, a cikin Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma Zuwa Harshen Hausa, shafi na 513, ya ce, “Babu kunci a cikin Musulunci. Duk inda aka fadi tsanani kuma an fadi yadda sauki zai samu a kowane hali.”
(3) Allah Ya ce wa Annabawa, a daidaikunsu, “Ka kira Ni (ka roke Ni) Zan amsa maka,” su kuwa al’ummar Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, sai aka kawo wannan aya ta 60 da ke cikin Sura ta 40 (Ghaafir), aka danganta su da ita.” Ibnu Abiy Haatim ne ya ruwaito wannan babban matsayi da aka ba al’ummar Musulmi, wanda ba a ba kowace al’umma kafin ta ba.
Daga nan ne dai, sai a cikin shi tafsirin Ibnu Katheer din, aka kawo wancan hadisi da ya gabata, na cewa ita addu’a dai ita ce ibadah, sannan aka karanta wannan aya da ake magana a kanta. To, a can an nuna cewa Imam Ahmad ne ya ruwaito hadisin, amma a nan an nuna wasu daga cikin As’habus Sunan, wato Attirmdhi da An-Nasa’i da Ibnu Maajah da Ibnu Abiy Haatim da Ibnu Jarir, sun fitar da hadisin, wanda Imam Attirmidhi ya ba shi darajar “Hasan Sahih.” Haka nan Abu Dawud da Attirmidhi da An-Nasa’i da Ibnu Jarir sun fitar da hadisin da wani isnadi na daban.
Maganar da Allah Ya yi ta cewa, “Lallai wadannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama suna kaskantattu.” Wato wadanda suke jin kansu, wai sun fi karfin su roki Allah, Shi kadai, saboda girman kansu, suna nuna sun isa, suna takama da matsayinsu, lallai za su shiga wuta suna cikin kaskanci, suna wulakantattu, su koma ba kowan-kowa ba.
Imam Ahmad ya ruwaito wani hadisi daga Amru dan Shu’aibu daga babansa, daga kakansa cewa Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Za a tayar da masu girman kai, ranar Alkiyama, kamar kwatankwacin kiyashi a ganin mutane, sai duk halittu su yi ta tattake su don wulakanci (sai kamar ana kwallo da su) har su shiga cikin waji kejin wuta (ko gidan sarka), wanda ake kira ‘Bulas’, inda za a ciyar da su balbalin wuta kuma a shayar da su guggubin kazantar azabar mazinatan wuta, wadanda wuta ke shiga ta farjojinsu ta biyo ta wuto da guggubin kazantar cikunansu.”
An samo daga Abiy Hurairata, Allah Ya yarda da shi da ya ce, Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Duk wanda bai roki Allah, Mai girma da daukaka ba, to (Allah) Yana fushi da shi (ko Allah Ya yi fushi da shi).” Imam Ahmad ya kadaita da wannan hadisi, amma babu abin zargi game da wannan riwayar.
Haka nan Annabi, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Mafi falalar ibada, ita ce addu’a.” Sahihu Abiy Dawuda, hadisi na 1,284.
A karshe Annabi, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Addu’a tana amfanar abin da aka saukar da ma abin da ba a saukar ba, saboda haka gare ku ya bayin Allah game da mayar da hankali wajen yin addu’a.” An fitar da wannan hadisi a cikin littafi Sahihul Jami’u, hadisi na 2,635.
Muna rokon Allah Ya tsare mu daga girman kai har ta yadda ba za mu roke Shi ba. Allah Ya tabbatar mana da alheri a cikin roke-roken da muke yi maSa, jiya da yau da kuma abin da zai zo gaba, don girman ZatinSa.
Za mu dakata a nan, sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu, mu gabatar da muhimmanci da matsayin addu’a. Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!