✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Allah Ya yi wa surukar Atiku rasuwa

Matar tsohon Lamidon Adamwa Aliyu Musdafa kuma surukar Alhaji Atiku Abubakar ta rasu

Allah Ya yi wa matar tsohon Lamidon Adamwa, Dokta Aliyu Musdafa kuma surukar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar rasuwa.

Atiku Abubakar ne ya bayyana hakan a shafinsa na twitter inda yake mika saqon ta’aziyarsa ga iyalen marigayiyar.

“A madadina da iyalina ina mika sakon ta’aziyata ga Lamidon Adamawa Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa da kuma iyalen Musdafa tare da fatan Allah Ya jikanta da rahama”, Inji shi

Marigayiya Hajiya Khadija it ace matar tsohon Lamido da ta rage kafin rasuwarta, sannan it ace mahaifiyar Hajiya Rukayyatu mata ta uku ga Wazirin Adamawa Atiku Abubakar.

Rohotonni sun tadda mu cewa za’a yi jana’izarta a Yola da ke Jihar Adamawa.