✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Allah Ya yi wa Janar Mohammed Wushishi rasuwa

Janar Wushishi ya rasu yana da shekara 81 a Landan, inda yake kula da lafiyarsa

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi ya riga mu gidan gaskiya.

Iyalan marigayin sun ce ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan na kasar Birtaniya yana da shekara 81.

Janar Wushishi ya kasance Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya a Jamhuriya ta biyu, daga 1981 zuwa 1983.

An haife marigayi Janar Wushishi ne a shekarar 1940 a garin Wushishi, hedikwatar Karamar Hukumar Wushishi ta Jihar Neja.

A tsawon rayuwarsa ta aikin soji, ya rike mukamai da dama ciki har da Kwamandan Kwalejin Shugabancin Soji (CSC) da ke Jaji a Jihar Kaduna da kuma Babban Kwamandan Runduna ta 4 na Mayakan Kasa na Sojin Najeriya.