Shugaba Buhari ya ce Allah ne kadai zai iya samar da isasshen tsaro a kan iyakokin Najeriya da makwabciyarta, Jamhuriyar Nijar.
Buhari ya yi bayanin ne a ranar Talata yayin karbar bakuncin Shugaban tawagar ta kungiyar ECOWAS ta kafa domin sanya ido kan zaben Shugaban Kasa da ’Yan Majalisar Jamhuriyar Nijar, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Muhammad Namadi Sambo.
- ’Yan ta’adda za su kai hare-hare a lokacin Kirsimeti —DSS
- Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye matar aure’
A ranar ce kuma da Fadar Shugaban Kasa ta ce Najeriya na duba yiwuwar sake rufe iyakokinta na kan tudu guda hudu da ta bude a makon jiya.
Kakakin Shugaba Bahuri, Garba Shehu, ya ce gwamnati na duba yiwuwar sake rufe iyakokin ne saboda ’yan ta’adda da masu fasakwaurin makamai da safarar mutane na karakaina ta iyakokin da aka bude.
Bayanin na Garba Shehu wanda aka ya kasance bako a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin din Channels na zuwa ne mako guda kafin lokacin bude ragowar iyakokin.
Ya zargi kasashe makwabatan Najeriya da kin ba da hadin kai a dakile kwararowar ’yan ta’adda da kananan makamai, matsalar da ke kara rura wutar ta’addanci a kasar.
“Shi ne dalilin da ya sa a wancan lokaci Shugaban Kasa ya yanke shawarar rufe iyakokin har zuwa yanzu da aka bude su a makon jiya.
“Muna kara tattaunawa da makwabtanmu kan su bayar da hadin kai domin hana kwararowar ’yan ta’adda, makamai, muggan kwayoyi da kuma yin fataucin mata amma lamarin ya faskara sabanin tsammanin Shugaban Kasa.
“Za mu ci gaba da gwadawa mu gani, idan an cimma nasara, za a bude sauran iyakokin, idan kuma akwai matsala to dole Gwamnati ta sake nazari da yin karatun ta nutsu.”
A ranar Laraba, 16 ga wata Dasimban 2020 ne Najeriya ta sake bude wasu iyakokin ta hudu na kan tudu bayan rufe su a watan Agustan 2019.
Iyakokin sun hada da ta Seme a Jihar Legas, Illela a Jihar Sakkwato, Maigatari a Jihar Jigawa, sai kuma Mfun Jihar Kuros Riba.
Da suke ganawa game da zaben Nijar da ke tafe a watan Disamba 2020 da muke ciki, Buhari na yaba wa takwaransa na Nijar, Mahamadou Issoufou, saboda rahsin sauya tsarin mulkin kasarsa domin kara wa kansa wa’adin mulkinsa daga karo biyu.
Buhari ya kuma bayar da tabbacin ba wa Nijar duk taimakaon da ya kamata domin a samu
“Zan tattauna da Shugaban Kasar in yi masa tayin tallafin da za mu bayar.
“Muna bukatar yin duk abun da za mu iya domin a samu kwanciyar hankali a yankin Sahel.”
A nasa bangare, Namadi, ya bayar da tabbacin yin dukkan mai yiwuwa daga bangaren ECOWAS wurin ganin an yi sahihi kuma karbabben zaben cikin lumana a Jamhuriyar Nijar.