Ta’ala kadiri Ka ban lafiya
In rera waken zaman lafiya.
Ka ba ni hazaka har da fasaha
Gurin rera wakar zaman lafiya.
Tsira aminci su tabbata gun
Muhammadu Manzon zaman lafiya.
Ba shi kadai ba har da sahabbai
Da alu da matansa baki daya.
Ya bar wasiyya ga umma tasa
Su zanka shiri don zaman lafiya.
Ya zo da sako na jalla gare mu
Islam nufinsa zaman lafiya.
Jigo biyar ne inji Muhamman
Biyo ni ka ji su ga baki daya.
Farkonsu Kalmar Shahada ka gane
Biyayya ga Allah zaman lafiya.
Yarda da sakon Muhammadu shi ma
Yana kai ga turbar zaman lafiya.
Na biyyunsu Sallah na khamsu biyar ne
Da ba su yuwa sai akwai lafiya.
Ga Ramalana mu zan azuminsa
Kaza ba da Zakka zaman lafiya.
Cikon nasu Hajji ka je in da hali
Guzuri da hanyarka mai lafiya.
Sahabi ya ce ya Rasulu gaya min
Zan sam sawaba zaman lafiya?
In na rike su biyar babu kari?
Manzo ya ce har ka zam lafiya.
A gobe kiyama a saka a Jannah
Nan ne tukewar zaman lafiya.
Ta yaya Musulmi a yau sunka baude
Wa horo na Manzon zaman lafiya?
Su kafirta bayi da Kalmar Shahada
Suna rushe sakon zaman lafiya.
Wasunsu gama har makamai gare su
Gilla suke ba zaman lafiya.
A Yerwa da Bama da Baga da Gwoza
Banki, Chibok ba zaman lafiya.
Sukan harbe mata da yara da tsofi
Samari su sace su baki daya.
Sukan sace mata da ba su da aure
Su auresu karhan suna fariya.
Su je makaranta su kona ta kurmus
Da yara cikinta ga baki daya.
Su ce musu arna da Kalmar Shahada
A baki, su fille su ba yafiya.
Boko Haramunga sun mana illa
Sun ci amanar zaman lafiya.
Sun watse birni kaza har da kauye
Kowa ta kai nai yake tafiya.
Iyali su watse da dangi hakan nan
Kowa a firgice sai tafiya.
Da muggan diya cikin namu soja
Ba su da niyyar zaman lafiya.
A kauye birane misalin su Baga
Sun yi ta gilla ga baki daya.
Sun kashe yara, sun kona mata
Sun kau da dadin zaman lafiya.
Ta’ala Mashiryi ga ni gare Ka
Ina zanka rokon zaman lafiya.
Gare ni da ’ya’ya da mata dukkanmu
Da dangi abokai ga baki daya.
Musulmi, Kirista Ta’ala Karimu
Hada mu zumuncin zaman lafiya.
Dade mu fahimta ta juna mu gane
Cikin arziki ba kamar lafiya.
Fitinnu na baya kaza na zamanu
Ka kare mu Jalla mu zam lafiya.
Mu rungumi ilmu na dini da dunya
Ci gaban rizku don zaman lafiya.
Dade mu da tsoronKa ya Jalla Sarki
Domin Muhamman mijin Mariya.
Ba mu kadai ba har da Boko Haramun
Yaranmu shirye su baki daya.
kanne da yayye cikinsu gaba dai
Maido su hanyar zaman lafiya.
Ka yafe su laifinsu komai yawansa
BayinKa ne Rabbu Mai lafiya.
Idan Ka tsane su Allahu Gafuru
Waye gare su ko a nan duniya?
Ka nunan da raina ina sintiri
Da nono a Yerwa zaman lafiya.
In je ni Bama in mika caffa
Gidan Mbusube Baba mai gaskiya.
Rabbi Ka kai ni Gwoza in gan su
Mutane na kirkin zaman lafiya.
Askira, Uba, Michika in je
kasashe na Margi mutan lafiya.
In shiga Maiha da Mubi in gan su
In ba su Wakar Zaman Lafiya.
In zo ni Gombi in shiga Hong
Har ma da Song don zaman lafiya.
Ku bar ni in zarce wajen Yola dangi
Filani na Lamido mai gaskiya.
In kwan salati in je ga Inna
Da “Intel” da dukkan maso lafiya.
Nuhu Ribadu aboki amini
Ina mika caffa ga mai gaskiya.
Da safe in je ni school in gane su
Teachers na ilmu cikin lafiya.
Ga yara da manya musamman ga mata
Ci gaba za mui ga baki daya.
In shiga mota in kama hanya
Zuwa Ganye gun su mutan lafiya.
In je ni in gana da danginmu Chamba
Da sarkinsu Gamwari mai gaskiya.
In zo ni Numan, in sheke ayata
Baki na Benuwai zaman lafiya.
Timawus Mathias in ganai har ya kai ni
Gurin nasa gwarzon zaman lafiya.
Sarkin ‘Bata in yi caffa gare shi
In fadi gu nasa mai gaskiya.
Lamurde zan sayi kifi gasasshe
Na cinye a mota zaman lafiya.
Ga Tula sun zo da tarba gare ni
Suna so in rera Zaman Lafiya.
Kaltungo, billiri har ma da Kumo
Ku tashi ku mike zaman lafiya.
Ku wo dandazon sallama don in gan ku
Ku ba ni aron kunnuwan lafiya.
Ku kore su Shaidan ku zan yin zumunci
Ku zauna ku mike cikin lafiya.
Zan shiga Kumo domin in gan shi
Muhammadu Kumo kana lafiya?
In ba su loto da baya tsawaita
Domin in zarce garin gaskiya.
Gombe ta Buba in sadu da dangi
Hausa da Fulbe ga baki daya.