A ranar Juma’a ne aka yi sallar jana’ar Shugaban Karamar Hukumar Gombe, Alhaji Aliyu Usman Haruna (Ali Ashaka) a Masallacin Juma’a na Fadar Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na III.
Ali Ashaka, ya rasu ne a ranar Laraba 6 ga watan Disamba a kasar Masar bayan ya yi fama da jinya inda sai a ranar juma’ar gawarsa ta iso Gombe don yi masa sallar jana’iza.
Babban Liman Masallacin Juma’a na Gombe Muhammad Pindiga shi ya jogaranci sallar inda Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da wasu manyan mutane, sarakuna da masu sarautar gargajiya da ’yan siyasa har ma da ’yan kasuwa da kuma daidaikun mutane suka halarci sallar daga ciki da wajen jihar
Kafin rasuwarsa, Ali Ashaka shi ne shugaban riko na Karamar Hukumar Gombe kuma Shugaban Kungiyar Shugabanin Kananan hukumomi na jihar Gombe.
- Harin Mauludi: Dole a yi adalci ga mutanen Tudun Biri —Sarkin Musulmi
- Kotun Ƙoli: APC da NNPP sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a Kano
Ya rasu yana da shekara 58 ya bar matan aure biyu da ’ya’ya shida.