✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alherin Allah ne kawai

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Madaukakin Sarki Mai komai Mai kowa, wanda cikin alherinSa ne muka kasance cikin masu rai a yau. Har abada…

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Madaukakin Sarki Mai komai Mai kowa, wanda cikin alherinSa ne muka kasance cikin masu rai a yau. Har abada babu wani wanda za a iya kwatanta shi da Shi; ko cikin duniya ko cikin sammai. Muna yi masa godiya domin irin wannan kauna da Yake nuna mana musamman a cikin shekarar da ta gabata. Akwai ababe da dama da suka auku, wadanda idan da Allah Ya bar mu kawai mu yi ta fama da su da warhaka, mai yiwuwa ba ma cikin wannan duniya. Asiri daya da Ubangiji Allah Ya bar wa kansa (sani) shi ne, sanin ranar mutuwarmu, ranar da za mu bar wannan duniya da dukan abin da ke cikinta. Wancan ranar; babu wanda zai iya ce ga shi, sai Allah da kanSa: ashe akwai dalilin da ya sa har yau muke cikin masu rai. Mutane da yawa ba sa lura da rayuwarsu ta yau da kullum; suna ganin kamar suna da iko a kan yau, wauta kan sa mutane su yi tunanin haka. 

Mun shigo sabuwar shekara ta 2015 kawai domin alherin Allah ne, babu wani a tsakaninmu da yake da tabbaci cewa zai ga mafarin wannan shekara; sai ga shi mun iske kanmu cikinta, wannan babban tagomashi ne daga wurin Allah Mai iko duka zuwa gare mu. Me ya kamata mu yi a lokaci kamar wannan? Kowane mai bi dole ne mu koma ga Ubangiji Allah cikin addu’a da kuma neman fuskarSa, domin mu san ko mene ne nufinsa game da mu cikin wannan shekara. Ya kamata mu zauna mu dubi yadda muka yi tafiya da Shi a bara, wane irin nasara muka ci; mu kuma ga inda muka yi kuskure; ba mu yi abin da Allah Yake so ba, domin mu iya gyara tafiyarmu da Shi a cikin wannan sabuwar shekara. Allah bai bar mu cikin duhu ba game da abin da Yake so mu yi maSa cikin rayuwa; Yana yin wannan kuwa ta wurin wa’azin da mu ke ji a kullum wanda bayinSa suna kawowa da kuma ta wurin yin binciken maganarSa. Mene ne muka yi kan umarnin da Allah Ya ba mu a shekarar da ta wuce? Mene ne kuma shirinmu cikin wannan sabuwar shekara? Za ka ci gaba da zama cikin zunubi ko kuwa za ka zo wurin Allah domin Ya yi maka jinkai? Za ka ci gaba da yin rashin biyayya ko kuwa za ka zama mai biyayya ga kowane umarnin Allah?
Wannan sabuwar shekara, shekara ce mai albarka kwarai da gaske; maganar Allah na koya mana cewa: “Gama na san irin tunanin da nake tunaninku da su, inji Ubangiji. Tunani mai lafiya, ba na masifa ba, domin in ba ku bege mai kyau a karshe. Sa’annan za yi ku kira gare Ni, ku tafi ku yi mini addu’a, ni ma in ji ku. Za ku neme Ni, ku same Ni kuma, lokacin da kuke nemana da zuciya daya.” (Irmiya: 29:11 – 13).
Haka nan kuma a cikin Littafin Ishaya: 43: 19, maganar Allah na cewa: “ Ga shi, zan yi wani sabon al’amari: yanzu zai bullo, ba za ku san shi ba? Har hanya a cikin daji zan yi; koguna kuma a cikin Hamada.”
Ina so ne in karfafa kowane mai bi da ya yi wannan karatun a yanzu. Allah da kanSa Ya ce, ya san irin tunanin da Yake da shi game da mu, yawancin lokaci mutum yakan ji kamar Allah Ya rigaya Ya yashe shi, domin bai ga biyan bukatunsa ba, ya yi ta yin addu’a amma har yau babu amsar wannan rokon Allahn da yake yi, sai ya karaya, ya ce wa kansa babu amfanin bin Allah kuma. Amma bari mu dubi inda muka yi karatu yanzun nan, Abu na farko shi ne:
Kowane dayanmu muna cikin tunanin Allah: Mai yiwuwa ne ka dade kana fama da wata damuwa, ka yi ta yin addu’a domin Allah Ya yaye maka shi, amma har yanzu kana ganin wannan matsala. Ka yi kuka sosai kana cewa yaushe nawa ranar za ta zo? Ka yi azumi duk da haka wannan kalubale yana nan daram, kamar ma bai yi motsi ba; a karshe sai ka ce a ranka: “Ina gani Allah Ya riga Ya manta da ni da kuma damuwata.” Idan haka ne tunaninka, to ga albishir, Allah bai manta da kai ba, bai kuma manta da damuwarka ba! Sau da dama muna so ne Allah Ya yi abu a namu lokacin, mukan manta cewa Allah Yana da lokacin da Yake yin abu; kuma ba Ya jan kafa ba Ya latti ko kadan, a daidai lokacin abu Yake yi.
Abu guda wanda Allah ke gaya mana ta wurin maganarSa shi ne lokacin da Allah Ya shirya domin Ya ziyarce ka ya iso, lokacin da Allah Yake so Ya share maka hawaye ya iso lokacin Ya yi kamar yadda Ya fadi a cikin Littafin Zabura: 102: 13 cewa “ Za ka tashi, za ka yi wa Sihiyona jinkai, Gama lokacin jin tausayinta ya yi, eh, ajiyayyen lokaci ya zo.” Ga dukan abin da Allah Yake yi akwai lokaci. Bisa ga alkawarin Allah, naka lokacin karbar tagomashi daga wurin Allah ya zo a cikin sunan Yesu Kiristi. Amin. Ubangiji Allah bai manta da kai ba ko kadan, kana nan cikin zuciyarSa. Allah Yana nan da kyakkyawan shiri domin dukan wanda zai dauki lokaci ya saurare shi. Ko a matsayinmu na kasa gabac daya, Allah Yana da kyakkyawar shiri domin wannan kasa Najeriya, idan har mun dauki lokaci domin neman nufinSa musamman game da zabe wanda shi ne babban abin da muke fuskanta a wannan kasa yau, da ba za mu fadi irin wasu kalmomin ba ko kadan. Kada mu yarda gaba ta shigo cikin al’ummar wannan kasa, domin kawai muna so a zabe mu a wani matsayi, idan mutane za su lizimta, su nemi nufin Allah, babu shakka Allah zai yi aikinSa.
Mene ne kake so Allah Ya yi maka a cikin wannan shekara da muka shiga? Kai fa wani irin tafiya kake so ka yi a cikin wannan shekara? Allah Yana son Ya yi mana alheri irin nasa, amma sai Ya ga irin tunanin da ke cikin zukatanmu. Duk abin da muke son mu aiwatar a wannan shekara masu yiwuwa ne musamman ma idan mun san yadda za mu zo gaban Allah cikin addu’a daga zuciya mai tsarki. Bari tsarkin zuciya da tsoron Allah da nuna kauna ga juna su zama abin da za su jagorance mu cikin dukan rayuwarmu.
’Yan uwana maza da mata, gudunmawar da kowanenmu zai iya bayarwa domin wannan kasa ta ci gaba ita ce ADDU’A. Surutu bai kawo riba ko kadan. Mu koma ga Allah, Shi kadai ke da asirin kan abin da muke bukata. Allah Ya taimake mu duka, Ya kuma ci gaba da tsare mu, amin.