A ranar Lahadi ne Mahajjata suka fara sauka a Mina gabanin halartar Tsayuwar Arafat a aikin Hajjin bana a Kasa Mai Tsarki.
Halartar aikin Hajjin a bana ya takaita ne ga maniyyata 60,000 mazauna Saudiyya wadanda kowannensu ya kammala daukar allurar rigakafin cutar COVID-19 kuma ba ya fama da wata cuta mai tsanani.
Aiki Hajjin na 2021 shi ne na biyu wajen karancin alhazai a zamanin cutar COVID-19, bayan na shekarar 2020 wanda mahajjata 10,000 suka halarta.
A shekarar 2019 alhazai sama da miliyan 2.5 ne suka halarci babbar ibadar kuma daya daga cikin shikashikan Musulunci wanda ake bukatar Musulmi ya yi akalla sau daya a rayuwarsa idan yana da hali.
Tun ranar Asabar mahajjata ke ta yin dawafi a Masallacin Harami da ke birnin Makkah a wani bangare na aikin Hajjin na bana.
Jigilar alhazai
Daga nan suke isa zuwa sansanin aikin Hajji da ke Mina mai nisan kilomita biyar daga Masallacin Harami, inda za suka kwana zuwa ranar 8 ga watan Dhul Hijjah (Yaumu Tarwiyah).
Zuwa ranar Lahadi an rika kawo mahajjata a cikin bas-bas din da aka cika rabinsu don kiyaya dokokin bayar da tazara.
Hukumomi sun kuma samar da motoci masu amfani da lantarki guda 3,000 don jigilar tsofaffi da wadanda ba sa iya zirga-zirga sosai.
“Mun bi dokar bayar da tazara a cikin sansanonin inda muka sanya mahajjata hudu kacal a kowane daki, mun kuma sanya shinge tsakanin kowane gado don tabbatar da tazarar.
“Ga wuraren taruwar jama’a kamar masallatai da gidan abinci a sansanin, mun sanya wani kamfanin tsaro wanda ya baza jami’ansa a cikin sansanin don tabbatar da cewa babu cunkoson jama’a,” inji mai kula da yawon bude ido, Hadi Fouad, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Tikitin zinariya
Aikin Hajjjin zai kai kololuwarsa a ranar Litinin inda mahajjata za su taru a Arafat, inda za su shafe tsawon yinin ranar suna ambaton Allah tare da addu’o’i har zuwa almuru.
A filin ne Dutsen Rahama, wanda kuma aka fi sani da Dutsen Arafat yake. Hadisai sun ruwaito cewa a dutsen ne Manzon Allah (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta karshe sama da shekara 1,400 da suka gabata.
Gabanin faduwar rana alhazan za su wuce zuwa Muzdalifa inda za su yi sallar Magriba da Isha sannan su kwana; Washegari (ranar Babbar Sallah) da hantsi za su koma Mina inda za su yi jifa, su yi yanka da kuma aski.
An zabi mahajjata 60,000 daga maniyyata sama da 558,000 da suka nemi gurbi a aikin Hajjin da aka kebance ga masu shekaru 18 zuwa 65.