✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Alhaji Buba Turaki, mahaifin ‘Singam’ ya rasu

Ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 10, maza 5 da mata 5.

Allah Ya yi wa Alhaji Buba Turaki, tsohon jami’in kwastam rasuwa da safiyar ranar Lahadi a Jihar Gombe.

Alhaji Buba wanda ya rasu yana da shekara 106 a duniya, shi ne mahaifin tsohon Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano CP Muhammad Wakili da ake yi wa inkiya da Singam.

Rashin lafiya ce ta yi ajalin Alhaji Buba Turaki kuma ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 10, maza 5 da mata 5.

Singam tare da mahaifinsa

Za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a kofar Fadar mai martaba Sarkin Gombe.

Cikin ’ya’yan marigayin har da tsohon kwamishinan ’yan sandan nan da ya yi fice a Jigawa da Katsina musamman a fagen yaki da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma matasan da ke shaye-shaye a Jihar kano.