✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Al-Shabaab ta kashe sojoji 30 a sansanin AU a Somaliya

Mayakan sun tayar da bama-bamai a wasu motoci kafin a fara musayar wuta.

Mayakan Al-Shabaab sun kashe akalla soja 30 a wani hari da suka kai kan sansanin sojojin wanzar da zama lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a Somaliya, inda aka gwabza kazamin fada.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, yayin da sojojin ke tsaka da aiki kuma an samu asarar rayuka a tsakanin bangarorin biyu.

Wani babban hafsan sojin Burundi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kimanin sojoji 30 ne suka mutu, wasu 22 kuma suka jikkata, yayin da wasu 10 suka bace; sai dai babu tabbaci game da adadin mutanen da aka kashe daga sojojin Somaliya ko na AU.

A wata sanarwa da mayakan suka fitar, sun ce sun karbe iko a sansanin bayan kashe sojojin AU 173, suka kuma fitar da wani bidiyo da ke nuna gawarwakin sojojin da suka kashe a kwance cikin jini.

Bayanai sun ce, rundunar sojojin na AU ta aike da helikwaftoci, bayan harin da mayakan na Al-Shebaab suka kaddamar kan sansanin sojojin wanzar da zaman lafiya daga kasar Burundi, a kusa da kauyen Ceel Baraf.

Kwamandan sojojin, Mohamed Ali, ya bayyana cewa mayakan na Al-Shebaab sun kaddamar da harin ne ta hanyar amfani da wata mota makare da bama-bamai, kafin daga bisani a fara musayar wuta tsakaninsu da dakarun na AU.

Wannan shi ne hari na farko da aka kai kan sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na AU, tun bayan da aka sabunta rundunar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somaliya tare da sauya mata suna daga AMISOM zuwa ATMIS a ranar 1 ga watan Afrilu.

Ana zargin mayakan Al-Shebaab kimanin 400 ne suka afka wa sansanin sojin bayan da suka tarwatsa wasu bama-bamai da motoci guda biyu.

Daga nan ne sojojin Burundin suka koma wani tsauni da ke kusa da wajen, inda suka ci gaba da fafatawa, tare da samun tallafin jirage marasa matuka da kuma helikwaftoci.