Dan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema, ya rattaba hannu na shekara uku a kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad da ke kasar Saudiyya.
Karim Benzema ya kawo karshen zamansa na tsawon shekara 14 a Real Madrid, idan ya zura kwallo 354.
- DAGA LARABA: Yadda Cire Tallafin Mai Ya Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya
- Muhimman abubuwa 10 da Gwamnan Kano ya aiwatar a kwana 10 na mulkinsa
Kungiyar Al-Ittihad ta sanar da daukar Benzema a matsayin dan wasanta a hukumance ne ta shafinta na Twitter a ranar Talata.
Benzema zai gana da tsohon abokinsa, Cristiano Ronaldo da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke Saudiyya.
Benzema ya kawo karshen zamansa a Real Madrid ne bayan tayi mai tsoka da sabuwar kungiyar tasa ta Al-Ittihad ta yi masa.
Real Madrid ta dauki Benzema a shekarar 2009 daga Lyon da ke kasar Faransa.
Shi ma gwarzon dan kwallon kafar duniya, wato Lionel Messi da zai bar PSG, ana sa ran zai koma Saudiyya da doka tamola.
Tuni wakilan kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke Saudiyya suka garzaya kasar Faransa don cimma yarjejeniyar daukar Messi.
Wakilan kungiyar sun shirya ganawa da mahaifin dan wasan George Messi don kammala cinikayyar dan wasan.