Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Nijeriya (JAMB) ta fitar da alƙaluman sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025, inda ta bayyana cewa yawancin daliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Litinin.
- Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus
- Yadda wani ya mayar da gadonsa motar hawa a Indiya
JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.
Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414.
A matakin maki tsakanin 250 zuwa 299 kuma, an samu ɗalibai 73,441 yayin da ɗalibai 334,560 suka samu maki tsakanin 200 zuwa 249.
Rukunin da ya fi yawan dal6ibai shi ne na maki 160 zuwa 199, inda aka samu ɗalibai dubu 983,187 wato kashi sama da 50 cikin 100 ke nan.
Haka kuma, ɗalibai dubu 488,197 suka samu maki tsakanin 140 zuwa 159, sannan dubu 57,419 suka samu tsakanin 120 zuwa 139.
Ɗalibai 3,820 kuma sun samu maki tsakanin 100 zuwa 119, sannan ɗalibai dubu 2,031 sun gaza samun ko da maki 100.