Za a ninka kudin kiran waya da sayen data a Najeriya karkashin tsarin Gwamnatin Tarayya na kara harajin amfani da waya a kasar.
Idan aka aiwatar da karin, ’yan Najeriya za su rika biyan N40 a kan kiran minti daya, maimakon kimanin N20; farashin data kuma zai iya kaiwa N2,500 a kan kowane gigabyte.
- NDLEA ta cafke dan bindiga mai shekara 90
- NAJERIYA A YAU: Yadda ‘IPOB’ Ta Yi Wa ’Yan Nijar 7 Kisan Gilla A Imo
- Fadar Shugaban Kasa ta koka bisa kisan dabbobinta
Aminiya ta gano cewa a kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin aiwatar da karin harajin kaso 5 cikin 100 a kan harkokin sadarwa, wanda hakan zai kara yawan harajin da ake biya a harkokin sadarwa zuwa kashi 12.5 cikin dari.
Masana a bangaren sadarwa sun ce sabon tsarin harajin, baya ga shafar masu amfani da waya ba ne kawai, zai kuma kara nauyin haraji a kan kamfanonin sadarwa wanda a karshe zai haifar da tsadar harkokin sadarwa.
Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta bayyana shirin ne a taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da haraji kan ayyukan sadarwa a Najeriya wanda Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta shirya.
Ta bayyana cewa harajin kashi 5 cikin 100 din yana cikin dokar kudi ta 2020.
Ta ce za a rika fitar da kudaden harajin da aka tara a kowane wata, ko kafin ranar 21 ga wata.
Matakin a cewarta, wani bangare ne na kokarin da Gwamnatin Tarayya na bunkasa kudaden shigar da ba na mai ba, sakamakon raguwar kudaden shiga, musamman daga bangaren mai.
Sai dai shawarar ta fuskanci suka daga Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantami.
Yayin da ma’aikatar kudi ta bayyana amincewar da shugaban kasa na aiwatar da sabon harajin kan harkokin sadarwa, kamar yadda dokar kudi ta tanada, ma’aikatar Pantami ta yi kakkausar suka kan cewa sabon harajin zai yi illa ga bangaren da masu amfani da wayoyi.
Daga Sagir Kano Saleh, Abdulaziz Abdulaziz (Abuja), Zakariyya Adaramola &Christiana T. Alabi (Legas)