Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi gargadin cewa matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu sassan Najeriya za ta iya sa wa a soke babban zaben 2023 da za a fara a watan gobe.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, wanda Shugaban Cibiyar Bincike Kan Harkokin Zabe (BEI), Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya wakilta ne ya yi gargadin ranar Litinin a Abuja.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron ba da horo kan shirye-shiryen tsaro a lokacin zaben.
Hukumar ta ce matsalar na iya sa wa a gaza gudanar da zaben a mazabu da dama, ta yadda zai yi wahala a iya bayyana wanda ya lashe shi, wanda ya ce hakan zai haifar da rudani a tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce, “Matukar ba a gano bakin zare tare da magance matsalar tsaro ba, akwai yiwuwar a fuskanci matsalar soke zaben a mazabun kasar nan da dama, ko kuma a dage shi, ta yadda ba zai yiwu a iya bayyana wanda ya lashe shi ba.
“Idan haka ta faru, za a fuskanci wata sarkakiya a tsarin mulkin Najeriya. Bai kamata a bari hakan ta faru ba.
“Saboda haka, ya zama wajibi jami’an tsaro da ma ma’aikatan zabe su yi taka-tsantsan da dukkan wani kaiwa da komowa a wajen zabe, sannan su kasance suna da isassun kayan aiki,” in ji Farfesa Mahmud.
Sai dai ya ce a kan haka, Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritaya) da Shugaban na INEC na aiki kafada da kafada wajen ganin an samar da ingantaccen yanayin da zai sa a gudanar da zaben cikin lumana.
Kazalika, Farfesa Mahmud ya ce maganar yin amfani da na’ura wajen aikewa da sakamakon zabe tare da dora shi a kan shafin hukumar ta hanyar amfani da na’urar BVAS na nan daram.