Tsohon shugaba kuma wanda ya kirkiri tsohuwar jam’iyyar CPC, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce akwai yarjejeniyar gemu da gemu cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai mika mulkin Najeriya ga tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu idan ya kammala wa’adinsa a 2023.
Hanga, wanda ya jagoranci daya daga cikin jam’iyyun da suka narke suka zama APC mai mulki a shekarar 2014 ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawarsa da Aminiya.
- Sau nawa aka taba soke gudanar da Aikin Hajji a tarihi?
- Layya: Wainar da ake toyawa a kasuwar raguna
Ya ce yarjejeniyar ce ma tasa Tinubun ya ci gaba da zama a APC bayan kammala wa’adin farko na Shugaba Buhari.
“Wannan wani sirri ne da yake a bayyane. Akwai yarjejeniya a kasa, kuma ko a doka wannan ba laifi ba ne. An cimma matsaya cewa in ya kammala wa’adinsa cewa zai mika wa Tinubu, wannan shine ma dalilin da yasa shi Tinubun bai fice daga jam’iyyar ba,” inji shi.
Sai dai Sanata Rufa’i Hanga ya bayyana kokwantonsa kan cewa APC za ta ba Tinubun tikitin takara a zabe mai zuwa, yana mai harsashen cewa akwai yuwuwar a sami baraka tsakanin jiga-jigan jam’iyyar daga bangaren gwamnoni da Fadar Shugaban Kasa.
Tsohon dan majalisar ya ce duk da yake duka manyan jam’iyyun suna da tarin matsaloli, akwai yuwuwar ’yan Najeriya su fi amincewa da PDP la’akari da irin kamun ludayin APC karkashin Buhari.
Fadar Shugaban Kasa da APC sun ki cewa uffan
Sai dai yunkurin Aminiya na jin ta bakin Fadar Shugaban Kasa da kuma jam’iyyar APC ya ci tura.
Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya ki ya mayar da martani a kan lamarin lokacin da wakilinmu ya tuntubeshi.
Kazalika, Sakataren riko na jam’iyyar APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe da Mataimakin Sakataren Yada Labarai, Yekini Nabena su ma ba su amsa kiran wayarsu ba.