Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da karkatar da kuɗin gwamnati da sunan tallafin man fetur.
Atiku ya ce ƙin amincewar da gwamnatin Tinubu ta yi na bayyana haƙiƙanin abin da take kashewa a kan tallafin man fetur ya nuna cewa tana karkatar da kuɗaɗen ne a sirri.
- Watan Babbar Sallah ya bayyana a Saudiyya
- Kotu ta sa ranar bayyana huruminta kan rushe masarautun Kano
Sai dai a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga, fadar shugaban ƙasa ta ce matsayinta kan tallafi bai sauya ba.
“Gwamnati na son jaddada cewa matsayarta kan cire tallafin man fetur ba ta sauya ba daga abin da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
“Zamanin tallafin man fetur ya ƙare.
“Ba a ware naira tiriliyan 5.4 kan tallafin man fetur ba a kasafin kuɗin 2024, kamar yadda ake ta raɗe-raɗi a kai”.
A yayin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke buga ƙirji da cewa ta janye tallafin man fetur da ya jefa al’umma cikin tsananin rayuwa, bayanan gwamnati na cewa an biya sama da Naira tiriliyan 5 da biliyan dubu 400 a matsayin kuɗin tallafin mai a wannan shekara ta 2024.
Daftarin rahoton da Ministan Kuɗi, Wale Edun ya miƙa wa Shugaba Tinubu a ranar Talata ya tabbatar da ƙarin Naira Tiriliyan 1 da biliyan dubu 800 kan tallafin shekarar 2023 na Naira Tiriliyan 3 da biliyan dubu 600.
Daftrin wani sabon tsare-tsare ne don magance manyan ƙalubalen da suka shafi bangare daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.
A baya dai, gwamnatin da Tinubu ke jagoranta ta tsaya tsayin daka cewa ba za ta ƙara biyan tallafin kuɗin man fetur ba.
Ko a watan Disamba, gwamnatin ta ce zamanin biyan kuɗin tallafin mai ya gushe a Najeriya, sabanin ikirarin da Bankin Duniya ya yi na cewa ƙasar na ci gaba da biyan tallafin.
Shi ma Ministan Yada Labarai, Mohamed Idris da yake zantawa da gidan talabijin na Channels ya ce shugaba Tinubu ya bayyana karara tun daga ranar farko da ya hau mulki cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.
A cikin watan Afrilu, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin Tarayya da kashe maƙudan kuɗaɗe a matsayin tallafin man fetur fiye da yadda ma ake yi a baya.