✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai fursunoni 3,298 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a Najeriya

"Rabon da a yanke hukuncin tun 2016 a Jihar Edo"

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta ce akwai akalla fursunoni 3,298 da aka yanke wa hukuncin kisa kuma suke zaman jiran a zartar musu da shi a gidajen kurkukun kasar.

Kakakin hukumar na kasa, Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Laraba a Abuja.

Ya ce galibi a Najeriya ba a cika zartar da hukuncin ba ga wadanda aka yanke musu ba.

Ya ce, “Akwai lokutan rashin tabbas yayin da wadanda aka yanke wa hukuncin suke daukaka kara zuwa kotuna na gaba.

“Fursunonin da ke jiran hukuncin kisa wasu daga cikinsu kan shafe kusan shekara 15 bayan yanke musu hukuncin.

“Muna da su da yawa a gidajenmu, ya zuwa yau, muna da 3,298 da suke zaman jiran a zartar musu da hukuncin. Adadinsu ya kai kusan kaso 4.5 cikin 100 na fursunonin da suke gidajen yarin Najeriya,” in ji shi.

Ya ce da yawa daga cikin irin wadannan fursunonin sun aikata munanan laifuka ne irin su kisan kai, fashi da makami da ta’addanci da dai sauransu.

Sai dai ya ce a baya, an sami nasarar zaratr da hukuncin kisan ga mutane da dama, kafin kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dan Adam su dada yin yawa sosai.

“Kodayake har yanzu ana yi, amma ba kasafai ake gani ba. Rabon da a aiwatar wa da wani fursuna hukuncin kisa tun a shekarar 2016 a Jihar Edo,” in ji Kakakin. (NAN)