✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano

An shirya musabakar ce da nufin sauya tunanin fursunoni domin su zamo mutane da al'umma za ta amfana da su bayan sun kammala zaman gidan…

Wasu fursunoni uku da ke tsare a gidajen yari daban-daban sun lashe Gasar Musabakar Al-Kur’ani da aka gudanar a Jihar Kano.

Fursunoni sun lashe gasar da Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta shinrya a matsayin wani bangare na tsarin ilimin fursunoni.

An shirya musabakar ce da nufin sauya tunanin fursunoni domin su zamo mutane da al’umma za ta amfana da su bayan sun kammala zaman gidan yari.

Mai magana da yawun hukumar gidajen yari a Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce an shirya musabakar ce domin kyautata halayyar masu zaman gidan yari.

Ya bayyana cewa furunan da ya lashe gasar yana tsare ne a gidan yarin Kumawa, inda ya samu kyautar Naira dubu dari.

Na biyu kuma a Gidan Yarin Goron Dutse yake tsare, kuma shi ma ya samu kyautar Naira dubu 50. Mutum uku yana tsare ne a Gidan Yarin da ke Janguza kuma ya samu kyautar Naira dubu ashirirn.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Kungiyar Alarammomi, Gwani Shuaibu Shehu, ya yaba wa Kwamnturolan Hukumar Gidajen Yari na Jihar Kano kan zurfin tunaninsa wajen shirya musabakar.

Ya kuma yaba masa da sama wa tsararrun wuraren da suka dace domin gudanar da al’amuran addini da sauran abubuwan da za su inganta rayuwarsu.

Gwani Shuaibu ya kuam yaba wa Ko’odinentan hukumar kan harkokin addinin, DSC Murtala Nasidi Kabara bisa yadda suke koyar da fursunonin karatun Al-Kur’ani..

A nasa jawabin, Kwanturolan hukumar, Ado Inuwa ya bayayan godiyarsa ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II bisa halartar gasar musabakar da kansa.