Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce neman afuwar ‘yan Najeriya da Jam’iyyar PDP ta yi bai wadatar ba, har sai sun dukufa da addu’ar neman gafarar zunuban nasu ga Allah Ta’ala.
Bafarawa wanda ya bayyana haka a yayin gangamin PDP da yankin Arewa maso Yamma ya shirya a Katsina a makon jiya, ya ce, “Domin sabon Allah ne ‘ya’yan Jam’iyyar PDP suka aikata ga Mahaliccinsu wanda kuma zai iya azabatar da su a kansa idan ba su tuba ba.”
“Allah Madaukakin Sarki ba ya kuskure cikin al’amuransa, kuma wannan shi ne dalilin da ya sanya da PDP ta saba masa sai Ya karbe mulkin daga hannunsu Ya bai wa APC,’’ in ji shi.
Haka shi ma da yake jawabi a yayin gangamin, Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya ce suna fatan ‘yan Najeriya su sake maida mulki ga PDP a badi ta hanyar kada mata kuri’unsu baki daya kasancewar jam’iyya mai mulki ta APC a cewarsa ta gaza, sannan kuma ta kunyata ‘yan Najeriya. Yana mai cewa “APC ba ta da wani dalili na sake dawowa kan mulkin kasar nan sam.”
Ita ma Shugabar Mata ta kasa ta jam’iyyar, Hajiya Maria Umar Waziri ta bayyana cewa irin tururuwar da magoya bayan PDP suka yi a wannan gangami, duk da cewa a yanzu haka Shugaba Buhari na ziyarar karshen mako a mahaifarsa Daura, hakan na nuna irin karfi da tasirin da PDP ke da su a Katsina, duk da cogen da APC ke yi na cewa Katsina ba ta da ‘yan hamayya. Don haka ta ce “idan har muka fadi zabe Katsina a 2019, to hakika aringizo aka yi mana.”
Haka zalika shi ma Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema ya karayata zargin rashawa da gwamnan Katsina mai ci, Aminu Bello Masari ya lika masa, don biyan wata bukata ta kashin kai kawai. Ya ce: “Dimokradiyya batu ne na zabi; ka zabi jam’iyyarka a baya. Amma yanzu lokacinmu ne mu zabi zabinmu a zabe mai zuwa. Na bar zunzurun kudi har Naira Biliyan 14.5 a cikin asusun jihar nan,amma sun ce ba gaskiya ba ne, Na inganta ilmi da gine-gine, sun ce ba gaskiya ba ne bashi na karbo, amma har gobe ina kalubalantar ko ma waye, da ya kawo hujjarsa karara akan wadannan zargi idan ya isa.’’
Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, su fita batun neman wani matsayi a maida hankali wajen yin aiki kawai don cimma nasarar jam’iyyar a 2019. Domin a cewarsa babu wata nasarar da za a iya samu ba tare da hadin kai ba.