Babban mai ba da shawara ta musamman kan harkokin tsaro ga Gwamnan Jihar Yobe, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya ya nuna rashin jin dadinsa bisa karancin samun mata ’yan asalin jihar suna shiga aikin soja.
Birgediya Janar Dahiru wanda ke zaman Shugaban Kwamitin Kula da Tantancewa da Daukar Sababbin Jami’an Tsaro na Jihar Yobe, ya ce a dalilin haka ne yake rokon mata da su rika shiga aikin soja don a dama da su.
- Boko Haram ta sake kai hari, ta yi ta’asa a garin Chibok
- Abin da ya sa aka tsere wa matan Hausawa a harkar kasuwanci
Birgediya Janar Dahiru ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a cibiyar daukar sababbin sojoji da ke barikin Soja na Bataliya ta 241 da ke garin Nguru a Jihar Yobe ya yin gudanar tantance sababbin sojojin.
A cewarsa, “akwai bukatar iyaye su rika barin ’ya’yansu mata suna shiga aikin soja, domin mun yi imani cewar, addini da al’adunmu ke sa da wuya a wannan bangare na kasa mata su iya jure shiga aikin na soja.”
Daga nan sai ya kwatatanta aikin tantance sababbin sojoji a matsayin irin wanda ya fi nagarta fiye da duk wani aikin tantancewa na masu damara.