Kulob xin Akwa United da yanzu haka yake rike da kofin Super Four kuma yake shirye-shiryen tunkakar kakar wasa ta bana da ake sa ran farawa a jibi Lahadi ya faxa cikin mawuyacin hali bayan Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta umarci ya biya tshon xan kwallonsa mai suna Menshack Chukwukem da kuma dillalinsa Ojore Oka bashin da suke bin kulob xin na Naira miliyan biyu da rabi ko kuma ya fuskanci fushin hukumar.
Tuni hukumar ta umarci NFF ta zaftare maki uku daga cikin adadin makin da kulob xin zai samu a gasar firimiya ta bana muddin bai biya xan kwallon da kuma ejent xinsa waxannan kuxi ba kafin a fara kakar wasa ta bana.  Bayan haka kuma akwai yiwuwar hukumar za ta hukunta kulob xin idan bai cika sharuxan da aka gindaya masa ba.
A bara ne dai FIFA ta umarci hukumar NFF ta binciki dambarwar rashin biyan xan kwallon da kuma ejent xinsa waxannan kuxaxe bayan yarjejeniyar da suka kulla da shi.  Hakan ta sa hukumar NFF ta kafa kwamitin bincike kuma ta samu kulob xin da laifi inda ta rubuta masa wasika a ranar 6 ga watan Janairun 2015 don ganin ya biya xan kwallon da ejent xinsa hakkokinsu.  Ganin har yanzu kulob xin bai biya su ba ne ta sa FIFA ta xauki wannan mataki.
Yanzu dai kulob xin ya shiga tsaka mai wuya a bisa sharuxxan da FIFA ta gindaya masa.
Akwa United ta faxa komar Hukumar FIFA
Kulob xin Akwa United da yanzu haka yake rike da kofin Super Four kuma yake shirye-shiryen tunkakar kakar wasa ta bana da ake sa ran…