Ministan yankin Neja Delta, Godswill Akpabio ya musanta zargin da ya yi wa ‘yan Majalisar Tarayya na karbar kashi 60 cikin 100 na kwangilolin Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).
Ya ce Majalisar ba ta fahimci abin da yake nufi a bayanin da ya yi ba a lokacin binciken da ta ke yi a kan zargin karkatar da biliyan N40 a NDDC.
“Game da kashi 60 na kwangilolin da na yi, kwamitin binciken bai ba ni damar yin bayani ba; kuma ni amsa na bayar ga tambayar daya daga cikn ‘yan kwamitin”, inji shi.
A wasikarsa ga Majalisar Wakilai wadda ta ba shi wa’adin awa 48 ya wallafa sunayen ‘yan majalisar da suka karbi kwangilolin, a ranar Alhamis, Akabio ya ce shi ba zargin da ya yi ba ke nan.
A lokacin da ministan yake bayani a gaban kwamitin bincike na Majalisar kan zargin facaka da biliyan N40 a NDDC, ya yi zargin cewa ‘yan majalisa ne ke karbar yawancin ayyukan hukumar wadda ke karkashin ma’aikatarsa.
Lamarin ya sa babban zauren majalisar ba wa ministan kwana biyuya bayyana sunayen wadanda NDDC ta ba wa ayyuka ko kuma ta daure shi.
A ranar Alhamis 23 ga watan Yuli ne wa’adin da majalisar ta ba wa ministan ke karewa.