Kungiyoyin fararen hula da masu sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya sun caccaki Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio.
Sanata Akpabio na shan caccakar ne kan kalaman da ya yi na cewa yana zargin ba ’yan kasar nan ba ne suka yi wa sojoji kisan gilla a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Jihar Delta.
An jiyo Sanata Akpabio na cewa, “Fatan da ya kamata mu yi yanzu shi ne a tsaurara bincike kan gaskiyar waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki.”
Ya ce “a sanina mutanen Delta na mutunta duk mai sanya kayan sarki, don haka ba zan so tashi guda in yarda cewa ’yan wannan yankin ne za su rufe idonsu su kashe sojojin Najeriya ba.”
Wannan kalamai da Akpabio ya yi a zaman majalisar ranar Talata sun tada kura, inda tuni ƙungiyoyin fararen hula da ’yan Najeriya, da masu sharhi a kan harkokin tsaro suka dira kan Sanatan da martani iri-iri.
- Ya sa an yanke kafafunsa don samun kuɗin inshora
- Ina tsammanin baƙi daga ƙetare ne suka kashe sojoji a Delta — Akpabio
‘Kalaman Akpabio abin takaici ne, kuma abin a yi Allah wadai ne’
Da yake martani ga kalaman na Sanata Akpabio, Auwal Musa Rafsanjani, babban darakta a Cibiyar Bayar da Shawarwari kan Dokokin da za su shafi Jama’a (CISLAC) ya ce kalaman abun Allah wadai ne.
“Kalaman Shugaba Majalisar Dattawan Najeriya sun yi muni, kuma abin a yi tir ne.”
Ya ce, “Mai laifi a ko’ina ya ke mai laifi ne, bai dace Sanata Akpabio ya nemi wanke waɗanda ake zargi da aikata wannan ɗanyen aiki ga dakarun tsaron kasar nan ba.”
A nasa bangaren, Tunde Salman, na wata kungiya mai rajin kawo tsarin shugabanci nagari a Najeriya, ya yi tir da waɗannan kalamai na Shugaban Majalisar Dattawan
Ya ce, “wadannan kalamai sun yi muni, kuma dole a zakulo waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki a hukuntasu.”
‘Akpabio ya faɗa mana ‘yan ina ne suka kashe mana sojoji’
Babban darakta a CLEEN Foundation, Gad Peter cewa ya yi, “ya kamata masu riƙe da muƙamai na siyasa su riƙa sanya wa bakinsu linzami idan an samu faruwar irin wannan mummunan lamari
“Tunda ya ce baƙi ne daga ƙetare suka kawo wa dakarun sojinmu hari, sai ya faɗa mana ‘yan ina ne domin mu afka musu da yaƙi, tunda sun taba mu gaskiya.”
A fahimci Akpabio — HURIWA
A nasa bangaren, Emmanuel Onwubiko, Ko’odineta na Kungiyar Marubuta Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya (HURIWA), ya ce: “Kalaman Akpabio hasashe ne kawai. Don haka, yana iya zama daidai kuma yana iya kuskure.”
“Mai yiwuwa abin da yake nufi da baƙi daga ƙetare shi ne wata kila ‘yan wasu jihohin Najeriya ne suka aikata wannan danyen aikin ba asalin jama’ar Delta ba.”
Tuni dai majalisar wakilai da ta dattawan da gwamnatin Jihar Delta suka kafa kwamitocin bincike da zakulo waɗanda suka yi wannan aika-aika, a daidai lokacin da ake fama da matsalolin tsaro iri-iri da buƙatar ƙarin adadin soji a Najeriya.
Haka zalika shugaban kwamitin tsaro a Majalisar Dattawan, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana wannan al’amari a matsayin wani takalar faɗa ga bangaren tsaron kasar nan da kuma yunƙurin tunkaɗe tubalin zaman lafiya a yankin.