Akalla mutum 600 ne har yanzu ake nema bayan zaftarewar lakar da ta zo hade da ambaliyar.
Shugaba Ernest Bai Koroma ya ayyana kwana bakwai a matsayin ranakun gudanar da alhini, da kuma bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.
Hukumar agaji ta Red Cross, ta yi gargadin cewa ya kamata a hanzarta neman mutane kafin su mutu.
Kakakin fadar shugaban kasar Abdulai Baraytay, ya shaida wa BBC cewa ana ci gaba da tsamo gawawwaki daga cikin lakar.
Duk da haka dai, ana shirin gudanar da jana’izar bai daya a ranar Laraba, domin rage gawawwakin da ke dakunan ajiye gawawwaki a asibiti.
BBC ta ruwaito cewa masu aikin agajin sun galabaita matuka saboda tsananin aikin da suke yi na ganin sun ceto jama’a.